Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da ɓarkewar cutar Kwalera a jihar inda cutar ta yi ajalin mutum 10 a ƙaramar hukumar Mubi.
A ranar Laraba a garin Yola yayin da yake ganawa da manema labarai kwamishinan lafiyar jihar Feliɗ Tangwami ya ce duk mutanen da suka mutu a dalilin cutar sun mutu ne a gida a maimakon asibiti.
Tangwami ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar ƙungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO sun ɗauki matakai domin daƙile yaɗuwar cutar.
“Tun da cutar ta ɓarke muke ƙoƙarin mu wajen ganin mun daƙile yaɗuwar cutar.
Kwamishinan ya ce mutanen da suka kamu da cutar da suka je asibiti sun samu sauƙi inda a ranar 4 ga Nuwanba akwai mutum 25 dake asibiti suna karɓan magani sannan da dama an sallame su bayan an wayar da kansu kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Ya ce shugaban fannin daƙile yaɗuwar cututtuka da wakilan fannin daƙile yaɗuwar cututtuka na Hukumar NPHCDA na Mubi domin gudanar da bincike kan yaɗuwar cutar tare da wayar da kan mutane mahimmancin kiyaye tsafta domin guje wa kamuwa da cutar.
A dalilin binciken da suka gudanar jami’an lafiyar sun fara gano wasu daga cikin mutanen da suka kamu da cutar domin tabbatar da cewa sun samu maganin cutar.
Tangwami ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su mara wa gwamnati baya wajen wayar da kan mutane mahimmancin gaggauta zuwa asibiti da zaran sun fara rashin lafiya.
Ya kuma ƙara jadadda muhimmancin tsaftace muhalli, abinci da jiki domin guje wa kamuwa da cutar.
