Al’ummar duniya na ƙara nuna goyon bayansu ga Falastinawa – Abu Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh ya bayyana cewa, al’ummar Falastinu suna kara samun goyon baya daga duniya, inda ya ce, a rana ta 230 da fara kisan ƙare dangi, an fara yaɗa irin munanan kisan kiyashi da ake yi wa al’umma Falastinu a gidajen talabijin na duniya.

Abu Shawesh ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce, tun daga ranar Al Nakba zuwa kisan kiyashin da ake yi a yanzu, shekaru 76 kenan, Falastinawa na cigaba da fuskantar gallazawa da rashin adalci da rashin jin daɗi da.

Ya qara da cewa, “ya zuwa ranar 22 ga watan Mayu, an sami shahidan Falastinawa 35,647, da jikkata 79,852, da wasu mutane 10,000 da suka ɓace. Ya kamata a lura cewa kusan kashi 72 daga cikinsu mata ne da yara.

“Kusan kashi 78 cikin 100 na al’ummar zirin Gaza a yanzu suna fuskantar barazana kaura daga sojojin Isra’ila.

“Kamfanonin burodi guda biyar ne suka rage a duk faɗin Gaza. Kusan wasu goma sha biyu kuma sun daina aiki saboda ƙarancin mai da kayan aiki.

“Tun daga ranar 7 ga Oktoba zuwa 19 ga watan Mayu, adadin wacanda ake tsare da su ya kai 8,775. Dukkan fursunonin Falastinawa suna fuskantar musgunawa, yunwa, rashin kulawar lafiya da kuma sauran hanyoyin azabtarwa da matakan gallazawa na Isra’ila,” inji Shawesh.

Ya ce, “Muna kira ga kwamitin qasa da qasa na Red Cross, Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Kare Haƙƙoƙin Ɗan Adam da su yi adalci tare da gudanar da ziyarar aiki na lokaci-lokaci ga fursunonin Falastinu don tabbatar da cewa an yi musu magani daidai da buƙatun dokokin ƙasa da ƙasa ba yadda Isra’ila take yi ba.”

“Ya zuwa ranar 11 ga Mayu, mutane miliyan 1.7 (sama da kashi 75 cikin 100 na al’ummar qasar) sun rasa matsugunansu a duk faɗin zirin Gaza. Ya zuwa ranar 12 ga Mayu, adadin abokan aikin UNRWA da aka kashe tun farkon tashin hankali ya kai 189, adadin da ya qaru daga rahoton da ya gabata.”

Yayin wata sanarwar haɗin gwiwa ranar Laraba, ƙasashen Sifaniya, da Norway, da Ireland suka bayyana shirinsu na amincewa da ƙasar Falastinawa mai cin gashin kanta a ranar 28 ga watan Mayu.

Shugabannin Falasɗinu sun yi maraba da wanna mataki, har ma hukumar Falasɗinawa ta PLO ta siffanta shi da “lokaci mai cike da tarihi”.

Ƙasashen da suke goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa na da imanin cewa hakan zai taimaka wajen ciyar da tattaunawar zaman lafiya gaba tsakanin Isra’ila da Falastinawan.

Sai dai kuma, borin kunya ya saka Isra’ila ta mayar da martani cikin fushi tana mai cewa za ta gayyaci jakadun ƙasashen uku don ta nuna musu bidiyon hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba da mayaƙan Hamas suka kai cikin kasarta.