Amfanin tazargade ga lafiyar iyali

Daga BILKISU YUSUF ALI

Anti Bilkisu, muna son mu ji amfanin tazargade ga lafiyar iyali.

Tazargade tana da matuƙar amfani a zamantakewar iyali hasali ma a shekarun baya zai yi wahala ka shiga gidajen Hausawa ba tare da ka tarar da an yi tanadinta ba don magance larurori na jiki ko na al’ada. Hausawa na amfani da ita don magance cutoci mabambanta. A wani nazari da Farfesa Bunza ya yi ya bayyana ana amfani da tazargade don:-

-Magance larurorin ciki, kamar matsalolin dattin ciki da kumburin ciki da ƙugin ciki wanda ake haɗa ta da tsamiya da gauta a sha.

-Ana jikata kaɗan a sha bayan cin abinci don magance larurorin maiƙo.

-Ana amfani da tazargade don inganta garkuwar jiki.

-Tana amfani wajen sa mutum ya yi bacci me kyau.

-Tazargade tana da tasiri sosai wurin gyara al’aurar mace musamman ma ga wadda ta haihu ko kuma ta samu ƙari a dalilin haihuwa ko wani dalili na daban.

-Tana magani wurin kashe kwayoyin cututtuka da ake ɗauka a dalilin amfani da banɗaki marar kyau ko ta hanyar kusantar iyali (infection) daga irin wannan matsalar kan haifar da ƙaiƙayin gaba ko matse-matsi da warin gaba da fitar ruwa a gaban mace mai ƙarni ko wari da bushewar gaba. Haka shi ma namiji yake jin ƙaiƙayi da suka kamar ana tsira masa wani abu ko jin tafiya da sauransu.

Ga duk wanda ke da wannan larurar a na samun tazargade a tafasa ta ake kama ruwa da ita ko a shiga ciki a zauna kamar minti goma.

Ga mai tambaya ko ƙarin bayani yana iya tuntuɓar wannan layin, amma saƙo kawai, ko ta WhatsApp a 08039475191 ko kuma a shafina na Facebook mai suna Bilkisu Yusuf Ali.