Dukkanku makiyaya ne

Daga AISHA ASAS

Annabin rahma ya ce, “Dukkanku makiyaya ne, kuma Dukkanku abin tambaya ne a kan abin da ku ke kiyo.”

A yau shafin iyali zai yi tsokaci kan iyaye da ke facali da koyarwar Musulunci kan tarbiyar ‘ya’yansu. Sun ɗaura zanen aro da bai dace da addini da al’ada ta malam Bahaushe ba.

Cikin sauƙin da mu ka samu a matsayinmu na Musulmai, Musulunci ya bayyana mana komai na rayuwarmu, tun daga aure zuwa haihuwa da kuma tarbiyar ‘ya’yan da Allah Ya ba mu amanarsu. Hakan na nufin, addini bai bar mu kara zube ba.

Sai dai duk da yawaitar ilimi da sauƙin mallakar sanin duk abin da ya shige mana duhu, bai hana mu bin hanyar ɓata da sunan wayewa ba. Mun sakar wa zamani tarbiyar ‘ya’yan da suka kasance amana gare mu.

Tambayar da ya kamata iyaye su yi wa kansu ita ce, me za su gaya wa Allah a lokacin da suka tsayu gaban Sa, don bayanin yadda suka yi riƙon sakainar kashi da amanar da Ya ba su?

Rashin ba wa yara kyakyawar tarbiya tare da ɗora su kan tafarki madaidaici ne ƙashin bayan gurɓacewar matasa a wannan zamani.

Abin takaici a yanzu, iyaye ne ke tsoron ‘ya’yansu, saɓanin sananniyar al’ada ta bil adama. Abin haushe inji Bahaushe, wai nama na jan kare. Mun kai lokacin da ‘ya’ya ne ke shirya yadda zaman gidan iyayensu zai kasance, ta hanyar shimfiɗa buƙatunsu da suke so a bi. Idan kuwa hakan ta kasance, ta yaya ke uwa za ki hana ɗanki abin da ke buƙatar kwaɓa.

A yadda halittar mutum ta ke, ba wanda aka haifa da sani ko iyawa, idan ka cire wasu keɓanttatu da Allah ya bayyana, dukkanmu a doron ƙasa mu ke koya. Don haka ba ta yadda yaro zai san hanyar da ya kamata ya bi sai da taimakon iyayensa. Duk da cewa, duk wanda Allah ya shiryar zai zama na gari, duk da haka a farkon fari Allah ya ce ku ba su tarbiya, domin itace matakala zuwa ga shiriya.

A lokacin da kika ce ba kya son vacin ran ɗanki ya ke uwa, ko ba kya son wani ya faɗi aibunsa, ko ya masa hukunci, to kin sawwaƙa wa shaiɗan ƙudurinsa na ganin ya karkatar da ɗanki izuwa tafarkin ɓata.

Kamar yadda kuka sani, zuciya an halicce ta da son ababen da ke kusantata da nadama. Don haka tamkar kin ba wa ɗanki damar bin ɓatacciyar hanya da za ta cutar da shi wata rana.

Idan har iyaye za su tsaya tsayin daka, su ba wa ‘ya’yansu tarbiya daidai da koyarwar addinin Musulunci, su cika zukatansu da addini, da tabbas an wayi gari babu wani sauran tashin hankali da kashe-kashe a tsakaninmu. Da tabbas nagari za su rinjaye ɓata-gari, har ya kasance an wayi gari duk wani mai aikata assha zai zama mujiya a tsakanin mutane.

Iyaye ke da babban kaso a yawaitar ta’addanci tsakanin mutane, kuma su ke da babbar rawar da za su iya takawa don tsarkake al’umma mai tasowa.