Amurka ƙasa ce da har kullum take kitsa ƙarairayi

Daga CMG HAUSA

Kwanan nan ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar da wata sanarwa a shafinta na Intanet, inda ta shafawa wasu jami’an gwamnati gami da kafafen yada labaran ƙasar Sin bakin fenti. Tana mai cewa, wai sun ƙara ruwaito “bayanan bogi” na ƙasar Rasha kan batun Ukraine, al’amarin da ya taimakawa Rasha ɗaukar matakan soja kan Ukraine.

A cikin sanarwar, laifin da Amurka ta dorawa ƙasar Sin, rahotanni ne bisa gaskiya da ƙasar Sin ta ruwaito kawai. Alal misali, sanarwar ta zargi ƙasar Sin cewa, wai ta kara gishiri kan “bayanan ƙarya” da Rasha ta fitar, wato Amurka ta mallaki ɗakunan gwajin halittu a Ukraine. Amma haƙiƙanin gaskiya ita ce, tun tuni ita Amurka ta amince da wannan.

A watan Nuwambar shekara ta 2021, Amurka ta gabatar da bayanin aikinta ga babban taron ƙasashen da suka rattaba hannu kan “yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba”, inda ta amince cewa ta mallaki wasu dakunan gwajin halittu 26 a ƙasar Ukraine. A watan Maris ɗin bana, ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar da takardar dake nuna cewa, tana da “wuraren haɗin-gwiwa” 46 a cikin Ukraine.

Sanarwar ta kara da cewa, game da yadda ƙasar Sin ta yi don kara ruwaito “rahotannin ƙarya” na Rasha, za’a iya samun ƙarin haske ta jaridar New York Times da sauran wasu kafafen yada labarai, al’amarin da ya sake shaida cewa, jami’an gwamnati gami da kafofin watsa labarai na Amurka ne suke riƙa yada “labaran bogi” kan batun Ukraine, kuma ita ƙasar Sin tana jin raɗaɗi a jikinta saboda shafa mata baƙin fenti da Amurka ta yi.

Amurka, wadda ita ce ta ƙirƙiro rikicin Ukraine, ta rasa imani a duk faɗin duniya tun tuni. Duk wani abun da ta yi na shafawa ƙasar Sin bakin fenti, ya sake shaida mummunan laifin da ita kanta ta aikata.

Fassarawa: Murtala Zhang