Nijeriya ta tanƙwara Ingila ta ayyana ‘yan IPOB a matsayin ‘yan ta’adda

Daga AMINA YUSUF ALI

Bayan ɗaukar lokaci ana jayayya, a yanzu gwamnatin Ingila ta goyi bayan Nijeriya wajen ayyana ‘yan ƙungiyar Biafra (IPOB) na Nijeriya, a matsayin ‘yan ta’adda.

Wannan bayanin yana zuwa ne bayan shekaru 5 da kotun ƙoli ta tarayyar Nijeriya a Abuja ta ayyana ƙungiyar a matsayin ‘yan ta’adda a ƙasar.

Wannan hukunci da Ingila ta yanke na ayyana IPOB a matsayin ‘yan ta’adda yana ƙunshe ne a wani jawabi na ƙasar Ingila kan mafakar ‘yan gudun hijira, ta hannun ɓangaren kula da biza da shige da fice a ƙasar (UKVI) suka wallafa a shafinsu na yanar gizo.

A cikin jawabin da aka wallafa a cikin watan Mayun shekarar nan ta 2022, ƙasar ta bayyana IPOB da dakarunta na ESN a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci.

A cikin jawabin dai har’ilayau, Ingila ta zargi ƙungiyoyin IPOB da ESN da alhakin tayar da zaune tsaye da yi wa haƙƙin bil-adama a yankin kudu maso gabashin Nijeriya karan-tsaye. Saboda haka ne ƙasar ta ba da umarni ga jami’an samar da biza na ƙasar a kan su cire dukkan ‘yan ƙungiyoyin daga tsarinta na ba da mafaka ga ‘yan gudun hijira.

A baya da gwamnatin masarautar Ingila ta yi niyyar ba da mafaka ga ‘yan IPOB ga ‘yan ƙungiyar tabbatar da ƙasar Biyafara (MASSOB) da Nijeriya take tuhuma.

A wancan lokacin UKVI, ta ba da umarni ga masu ruwa da tsakinta da su taimaka wa dukkan wani mutum wanda yake fuskantar barazana ko tuhuma, ko cin mutunci ko ma ɗaurin a sakamakon bayyana goyon baya ga ƙungiyar IPOB. Idan har mutumin zai iya bayyana shaidar tuhumar da aka yi masa, to hukumar za ta ba shi mafaka a ƙasar Ingila.

Kodayake, Gwamnatin Ingila ta yi amanta kuma ta lashe kwanaki kaɗan bayan ba da wancan umarni. Hakan ya biyo bayan ƙorafi da gwamnatin Nijeriya ta turo. Inda Nijeriya ta bayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci sannan kuma dakarunta na ESN wacce aka kafa a Disambar 2020 sun aikata laifuffuka masu yawa na tauye haƙƙin bil-adama a Nijeriya.

A yanzu haka dai ƙasar Ingila ta cire IPOB ɗin daga jerin waɗanda za ta cigaba da ba wa mafaka. Haka ƙungiyar MASSOB ita ma an dakatar da ita, duk da dai ba a ayyana ta a matsayin ‘yan ta’adda ba, amma rahotanni sun nuna irin yadda suke ta da tarzoma tsakaninsu da jami’an tsaro a Najeriya.

Sai dai kuma, Gwamnatin Ingila ta bayyana cewa, idan ɗaya daga cikin ‘yan ƙungiyar ya zo neman mafaka, a matsayinsa na mutum, za a iya sama masa mafaka a ƙasar. Sai dai kuma in dai aka samu mutumin ko ma waye shi, yana da hannu a wajen tauye haƙƙin mutane, to ba za a taɓa ba shi mafaka ba a ƙasar.

Amma a cewar bayanin, kowaye baya ga waɗanda aka lissafa, ƙasar za ta iya tallafa masa idan buƙatar hakan ta taso. A kan wannan UKVI take ba da shawara ga masu ruwa da tsakinta da su kula da bayanin kowa a matsayinsa ba wai a ƙarƙashin kowacce ƙungiya ba.