Membobi 9 na majalisar dokokin Kano sun sauya sheƙa daga PDP zuwa NNPP

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Membobin majalisar dokoki na jihar Kano guda Takwas sun fice daga jami’iyyar PDP zuwa NNPP mai kayan marmari.

Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da mambobin majalisar suka fitar tare da ai kewa shugaban majalisar, Hon. Hamisu Ibrahim Chidari.

Takardar ficewar da shugabanta ya karɓa, sannan ya yi musu fatan alheri a sauyin shekarar da sukai.

Membobi takwas da suka sauya sheƙar daga PDP zuwa NNPP sun haɗa da:

1.Rt Hon. Isyaku Ali Danja da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Gezawa.

2.Hon. Umar Musa Gama mai wakiltar Nassarawa.

  1. Hon Aminu Sa’adu Ungogo daga Ungogo.
  2. Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa Dala.
  3. Hon. Tukur Muhd Fagge.
  4. Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dawakin Kudu.
  5. Hon. Garba Shehu Fammar Kibiya.
  6. Hon. Abubakar Uba Galadima Bebeji.
  7. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Kumbotso.

Sanarwar hakan na zuwa ne bayan da Daraktan yaɗa labarai na majalisar, Uba Abdullahi ya fitar kuma aka raba wa manema labarai ranar Juma’a a Kano.