Amurka: “Moriyata ta fi gaskiya”

Daga CMG HAUSA

Ƙasar Sin ta mayar da martani game da ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan.

Amma, wasu ‘yan siyasar Amurka suna ganin matakai masu dacewa da Sin ta ɗauka a matsayin waɗanda suka tsananta halin da ake ciki a yankin.

Yau “duniya a zanen MINA” na bayyana yadda ƙasar Amurka ke nuna girman kai a duniya.

A haƙiƙa, ƙasar Sin ta sha bayyana adawarta da ziyarar Pelosi a yankin Taiwan ta hanyoyi daban-daban a matakai daban-daban.

Kwanan baya, sakataren harkokin wajen ƙasar Antony Blinken ya bayyana cewa, Amurka ta nace ga kin yarda da balle yankin Taiwan daga ƙasar Sin, amma ba da daɗewa ba, ya manta da wannan batu, har ya zuga Pelosi da ta kai ziyara a yankin Taiwan.

Ganin yadda halin da ake ciki a yankin ya ƙara tsananta, sai suka dora laifi kan ƙasar Sin. Shin ba su san gaskiyar al’amarin game da yankin ba? A’a, suna sane sosai, amma a ganinsu, moriyarsu ta fi gaskiya.

A yau 10 ga wata, Sin ta gabatar da takardar bayani dangane da batun Taiwan da d’ɗinkuwar ƙasar Sin a sabon zamani, don ja kunnen mahukuntan yankin Taiwan da ma wasu ‘yan siyasar Amurka: dole ne su mutunta ikon mulkin ƙasar Sin, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar, kuma su mutunta gaskiya da yin watsi da girman kai.

Mai zane: MINA