Dauda Kahutu Rarara: Zakaran da Allah Ya nufa da cara

Daga KWAARED ABDU ZANGO

Haƙiƙa Allah shi ne gwani kuma mai ba wa kowa arziƙin da ya so ta hanyoyin da ɗan adam ya yanke ƙauna. Gaskiya ne akwai mawaƙa da yawa cikin duniyagga kuma ana ganin arziƙin da Allah Ta’ala yayi masu ta hanyar sana’ar waƙa.

Bari kawai mu duƙufa kawai a Nijeriya ta Arewa inda take da mawaƙa shahararru waɗanda sun yi fice sosai a duniyar waƙoƙin Hausa, kususan na zaɓe da masu sa hikimar su kaɗaita kotso, molo, garaya, kuntigi, goge da dai sauransu kamar kiɗan ɗanmaraya da mai irin muryarsa ɗan zamfara Babangida Kakadawa. To cikin mawaƙan nan akwai mawakan rubutattun waƙoƙi, wato masu waqa babu kiɗa kuma a wancan zamani akwai na siyasa kususan jam’iyyar talakawa ta Malam Aminu Kano, wacce aka fi sani da NEPU.

Gaskiya NEPU tana da zaƙaƙuran mawaƙa waɗanda suka yi suna ƙwarai da gaske wanda har zuwa PRP wacce ta ɓullo lokacin jamhiriya ta biyu. Ba sai an faɗa ba, domin a wancan zamani aka yi shahararren marubuci, kuma mawaƙin zube Dr. Sa’adu Zungur Allah Ya ji ƙansa, amin.

Haka akwai zaƙaƙurin mawaƙan rubutattun waƙoƙi kamar, Marigayi Dakta Abubakar Ladan wanda mutumin birnin Zaria ne, kuma ya shahara wurin waƙe shugabannin afrika nabda da kuma shiyyar da suka fito. Alhaji Abubakar Ladan ya yi wa PRP waƙa cewa “samarin ƙauye birni ku zaɓi Aminu ɗan talakawa”, waƙar ta yi armashi sosai duk da Malam bai so wasu daga cikin baitukan waƙar ba!

To koma me ake ciki dai, akwai mawaqa waɗanda Allah Ya ba su basira irin su Aminu Alan Waƙa wanda a yanzu tauraruwarsa take haske kamar gwanina wanda a dalilinsa na yi wannan rubutu wato Alhaji Dauda Kahutu Rarara Katsina. Gaskiyar lamari Alhaji Dauda Rarara ya fara waƙarsa ba ta siyasa ba ce, amma daga ƙarshe ya zama zaƙaƙuri wurin waƙoƙin siyasa wacce ta kai shi ƙoli a yanzu.

Gaskiyar lamari ba wai zuga wannan zaƙaƙurin mawaƙi nake ba, a’a gaskiya ce ta yi halinta inda wasu basu san cewa Allah Ta’ala shi ne mai raya ɗan jariri sabuwar haihuwa a daji ya rayu ya zama sarki ba, wannan Subhanahu Wata’ala ya yi ababe fiye da fahimtar ɗan adam domin shi ma yinsa ake yi ba tare da sanin shi kowaye ba.

Kaga dai Mamman Shata, wanda shi ma mutumin Katsina ne kuma shahararren mawaƙin Hausa, ga shi asalinsa Bafillace ne, a zamaninsa babu mawaƙin da ya shahara kamarsa cikin Duniyar waƙe na Hausa. Mawaƙa uku su sukafi kowa a Duniya su ne Alhaji Mamman Shata, Alhaji Muhammad Rafi na ƙasar India, sai kuma Sheikh Muhammad Wardi na Sudan.

To ashe mu ma zamu sami wani mawaƙin shahararre mai suna Alhaji Dauda Kahuru Rarara a lokacin da su waɗancan manyan mawaƙa suka koma ga mahaliccinmu, Allah Ta’ala Ya ji qan waɗancan musulmin mawaƙa waɗanda waƙoƙinsu ba su ƙirguwa, domin yawansu, abin mamaki dukkanninsu musulmi ne kuma daga sassan duniya daban-daban.

To haka Allah Yake ikonsa, sai wasu mutane su shahara ta wurin da ba a zato. Mu a nan Arewa ba safai muke ɗaukar mawaƙa da daraja ba, domin kawai ana ganinsu maroƙa ne, masu kalangu da molo, da sauransu duk da cewa suna faɗin abubuwa kamar dai azanci sai ka ga malamai a jami’oi suna amfani da su a ilimance.

To shi wannan bawan Allah da na yi wannan maƙala dominsa, wato Dauda Kahutu Rarara mutum ne da ya jawo wasu ƙananan mawaƙa kusa da shi domin taimaka musu, suma su yi irin tasu gwanintar a rayuwa.

Ganin haka ne ya sa su waɗannan ƙananan mawaƙa suke girmama Alhaji Dauda Kahutu Rarara domin ba shi da mugunta kuma sitidiyonsa kullum cike take da mawaƙa gwanaye, don haka kuma, shi ne suke kiransa da Ciyaman, wato shugaba; wannan kalmar yadda nake nanatawa saboda karamcinsa da nuna taimakon jama’a shi ne ladan gobe na kowanne irin bil adama.

Gaskiya, Alhaji Dauda Kahutu Rarara mawaƙi ne na siyasa, kuma ɗaukaka ta kai shi sama inda ta kaishi ƙoli sosai kuma har yanzu zarensa ƙara ƙwari yake yi kuma Insha Allah babu lokacin tsinkewa: Mutanen Kannywood, Sadi Sidi Sharifai Ahuwonku!

Alhaji Mamman Shata yake faɗi: “dila da kura da biri zaman dawa suka tara, amma halinsu ya bambamta.Ta Magaji mai ido ɗaya.

Kwamared Ibrahim Abdu Zango, Shugaban ƙungiyar Kano Unity Forum, Kano. 08175472298