Wai haka za mu zauna?

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI FAGGE

Ka ga mutum ya zo nan ƙiri-ƙiri yana ta haƙilon tsine wa Obasanjo ko Buhari ko Jonathan da sauransu amma sai ka gan shi in ɗalibi ne, an zana masa NECO ko WAEC ta hanyar cuwa-cuwa a “miracle centre” ko kuma ba shi da takardu na gaskiya, duk babu ne, ya biya an yi masa na ƙarya. Ko kuma ka gan shi ko ka gan ta a jami’a tana satar amsa, ko kuma a haɗa baki da shi a ƙara kuɗin da za a amsa a wajen babansa.

Idan magidanci ne yana koyarwa a jami’a ko a firamare ko a sakandire ka ga ba ya zuwa makaranta da wuri, in kuma ya je, ba ya gabatar da aikinsa yadda ya kamata, kuma ba ya jin komai.

Ko kuma in hedimasta ne ko firinsifal, ka ga yana karɓar kuɗin yara ta hanyar zalunci, ko kuma ba ya kula da ma’aikatarsa ko ma’aikatansa. Idan birkila ne ka ga yana sacewa wanda ya sa shi aiki siminti, ko kuma yana kokarin tauye mudun aiki, don ya zalunci wanda ya sa shi aikin.

Tun ba teloli ba, idan dai rashin cika alƙawari ne har ya zame wa wasunsu jiki, wasunsu kuma har su saci yadi.

Idan tantagaryar kwarafshan kuma kake so, to kawai jeka hukumomin KEDCO ko CAC ko NNPC ko Abuja da makamantansu, ko kuma azzaluman masu shari’a, ga su nan birjik!

Rashin mutunci kuwa, ka sami ‘yan siyasa ga tsabar sata. Rashin hankali kuma ka sami jahilan mabiya, wadanda idonsu yake rufewa, ko hauka ake yi, su ba ruwansu in dai maigidansu zai sato ya dan tarfa musu shikenan.

A rashin kula da aiki kuwa da rashin bin doka, kusan dukkanmu kanwar ja ce! Ga alqalai maha’inta ga lauyoyi maƙaryata ga akantoci azzalumai ga daliba daƙiƙai ga ‘yan bandits, waɗanda su har ma sun girmi kwarafshan sun koma kisa, don sun san su ba wanda zai kashe su.

To a hakan ne za mu dinga tsinewa wani. Ai in tsinuwa ce, duk mun san daga inda ya kamata a ce mun fara.

Gaskiya dai dukkanmu ya kamata mu gyara. Amma fa kai ni da kai da ke ne za mu fara gyarawa kafin mu ce wa wani ya gyara!

Allah dai Ya shirye mu kawai, Ya sa mu gane mu gyara, amin.

Muhammad Sulaiman Abdullahi Fagge ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi.