An ci tarar Joelinton tare da hana shi tuƙa mota

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An ci tarar ɗan ƙwallon Newcastle United, Joelington an kuma hana shi tuƙa mota shekara ɗaya, bayan samunsa da laifi tuƙi a cikin mayen barasa.

Mai buga wasa daga tsakiyar fili zai biya fam dubu 29, bayan da ya amince da laifin da aka tuhume shi tun farko.

‘Yan sanda sun tsare ɗan ƙasar Brazil a lokacin da ya ke tuƙa motarsa ta Marsandi kirar G Wagon ranar 12 ga watan Janairu a Ponteland Road, Newcastle.

Bayan da aka yi masa gwajin ko ya sha barasa ne aka same shi da laifin kwankwadar wuce kima da aka amince a yi tuƙin mota.

Wata kotun Majistare ce a Newcastle, ƙarƙashin mai shari’a, Paul Currer ta yanke masa hukuncin hana shi tuƙa mota zuwa shekara ɗaya.

Za kuma a iya rage hukuncin zuwa wata tara, idan Joelinton ya bi matakan da kotu ta gindaya masa sau da ƙafa.

Joelington, wanda ya koma Newcastle kan fam miliyan 40 a 2019, shi ne ya ci wa ƙungiyar ƙwallo a wasa da Southampton ranar Litinin a Carabao Cup ranar Litinin.

An taɓa cin tararsa fam 200, bayan da ya karya dokar kullen Korona, wanda ya ce zai je yin aski ne a lokacin.