Buhari ya naɗa kwamitin mutum 14 kan ƙarancin man fetur a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya amince da kundi na wani kwamiti mai mutane 14 domin tabbatar da samar da albarkatun man fetur da kuma bibiyar ƙa’idojin farashin man fetur.

Blueprint Manhaja ta tattaro cewa wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu amfani da albarkatun man fetur ke nuna ɓacin ransu game da taɓarɓarewar ƙarancinsa a cikin tashin farashin da ba a ƙayyade ba.

Yayin da wasu ’yan tsiraru a ɓangaren man fetur suka yaba da kafa kwamitin, wasu kuma sun ce shugaban da muƙarrabansa na fafatawa da lokaci.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Buhari wanda ke riƙe da mukamin Babban Ministan Man Fetur tun shekarar 2015 lokacin da ya ƙaddamar da majalisar ministocinsa zai jagoranci kwamitin gudanarwa da kansa yayin da laramin ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva shi ne mataimakin shugaban.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare ta Ƙasa; Babban Sakatare na Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tattalin Arziki; Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS); Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Ƙasa (NCS); Shugaban Hukumar Yaqi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) da kuma Kwamandan Rundunar Tsaron Karin Kaya ta Nijeriya (NSCDC).

Sauran membobin su ne Shugaban Hukumar, NMDPRA; Gwamnan Babban Bankin Ƙasa (CBN); Babban Jami’in Kamfanin NNPC Limited; Mai Bada Shawara na Musamman (ayyuka na musamman) ga Ƙaramin Ministan Man Fetur yayin da mai ba da shawara na fasaha na minista (tsakiyar) shine sakatare.

A cikin sanarwar da babban mai ba da shawara (kafofin yaɗa labarai) ya fitar ga Ƙaramin Minista, Horatius Egua, shugaban ya umurci NMDPRA da ta tabbatar da bin doka da oda da gwamnati ta amince da tsohon ma’aji da kuma farashin man fetur.

Ana kuma sa ran kwamitin zai tabbatar da kula da hajoji, da ganin an gyara matatun mai na NNPC Limited da kuma bin diddigin yadda ake rarrabawa yau da kullum don magance fasakwauri, a wani vangare na sharuɗɗansa.

Buhari ya kuma umurci kwamitin da ya tabbatar da tsarin kula da hajoji na ƙasa, da hangen nesa kan shirin gyara matatun mai na NNPC Limited da kuma tabbatar da bin diddigin albarkatun man fetur daga ƙarshe, musamman farashin don tantance yadda ake amfani da shi a kullum da kuma kawar da fasaƙwauri.