Shugaban Kasuwar Mile 12 a Legas ya kira taron zaman lafiya

Daga DAUDA USMAN a Legas

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne Shugaban Kasuwar Mile 12 a Legas, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Dallatun Egbaland) a Abeokuta ta jihar Ogun mazaunin cikin garin Legas ya kira taron neman ƙarin zaman lafiya da haɗin kawunan ‘yan kasuwar ta Mile 12 da kewayenta.

Taron wanda ya ƙunshi dukkannin al’ummar kasuwar da shuwagabannin ɓangarori da dattawan kasuwar da Yarabawa da sauran ƙabilu masu gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar gaba ɗaya.

Sakataren kasuwar Alhaji Balarabe Idiris ya jagoranci gabatar da taron kaɗan daga cikin shuwagabannin ɓangarorin kasuwar akwai Alhaji Abdullahi Tukur Kura, Shugaban ɓangaren albasa da Alhaji Bala Yaro Hunkuyi, Shugaban ɓangaren karas da kabeji da Alhaji Yahaya Bako, baki shugaban ɓangaren tattasai da tawagarsa.

Sauran sun haɗa Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano, Shugaban vangaren tumatiri da tawagarsa da Alhaji Muktar Jabo Shugaban ɓangaren busashen tattasai da dai sauran makamantansu.

Haka kuma kaɗan daga cikin dattawan kasuwar ta Mile 12 sun haɗa da Shugaban Ƙungiyar Dattawan Alhaji Isa Mohammed Mai Shinkafa da Alhaji Habu Faki (Garkuwan PFaki) da Alhaji Abdulwahab Tsoho Babangida da sauran makamantansu.

Da yake yin tsokaci a bisa kan wannan taron, Shugaban kasuwar ta Mile 12. Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam ya ce haƙiƙa sun kira wannan taro ne domin su gabatar da godiyarsu ga al’ummar kasuwar domin yauƙaƙa zaman lafiya da haɗin kan juna.

Alhaji Usman ya kuma gode wa mambobi da shuwagabannin kasuwar da suka bada goyon baya da amsa kiransu wajen goyon bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

sauran jawaban da suka gabata waɗanda suka fito daga bakunan iyayen kasuwar Alhaji Isa Mohammed da Alhaji Habu Faki Garkuwan Faki da Alhaji Abdulwahab Tsoho Babangida da sauran shuwagabannin ɓangarori waɗanda suka samu yin tsokaci a wajen taron dukkan jawabansu sun karkata ne a wajen kiraye-kiraye ga al’ummar kasuwar da su ƙara ƙoƙari wajen tsaftace harkokin kasuwancin su da ma kasuwar gabaɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *