An fara samun bayanai kan halin da tsohon shugaba Kabore ke ciki

Hamɓararren shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, yana cikin ƙoshin lafiya kuma sojoji suna tsare da shi a wani gida da ke fadar shugabancin ƙasar, kamar yadda wata majiya ta jam’iyyarsa ta bayyana.

Halin da Kabore da kuma inda yake ya zama muhimmin batu tun bayan da wasu sojoji suka hamɓarar da shi daga mulki a ranar Litinin, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ke jagorantar kiran da a sake shi.

A baya bayan nan ne kuma, wata majiya a jam’iyyar tsohon shugaba Kabore ta ‘People’s Movement for Progress’ MPP, ta tabbatar yana cikin ƙoshin lafiya, amma babu ƙarin bayani kan ko yana cikin halin ƙunci ko akasin haka.

Majiyar ta ƙara da cewar, Kabore na ƙarƙashin ɗauri ne na talala, ba a sansanin soji ba, zalika yana da likita, kuma yana da damar yin amfani da wayar salula, amma a cikin matakan sa ido.

A shekarar 2015 aka zaɓi Kabore mai shekaru 64, bayan boren da ya tilastawa Blaise Compaore barin mulki, wanda ya hau kan ƙaragar mulki tun shekara ta 1987.

An sake zaɓen Kabore a shekara ta 2020, amma a 2021 ya fuskanci fushin ‘yan ƙasar, sakamakon ƙaruwar hare-haren ‘yan ta’adda masu iƙirarin Jihadi da ƙarfin tsiya.

A ranar Litinin, Jami’an sojin Burkina Faso suka kama shugaban ƙasar Roch Marc Christian Kabore, wanda ya sha fuskantar zanga-zangar adawa daga dubban jama’a a kan gazawarsa wajen daƙile hare-haren ‘yan ta’adda a ƙasar.

A halin yanzu dai ƙasar da ke yankin Sahel tana ƙarƙashin ƙungiyar sojoji ‘yan Kjshin ƙasa ta MPSR, wadda Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ke jagoranta.