An farmaki ofishin Jaridar This Day bayan shekaru 10 da harin Boko Haram

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Wasu gungun mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari a ofishin kamfanin Jaridar This Day da ke Abuja, inda suka yi barazanar sheƙe dukkan ma’aikatan kamfanin.

Kafar Labarai ta Arise News, mallakin Kamfanin Jaridar This Day, ta ruwaito cewa, maharan da suke ɗauke da muggan makamai sun kutsa cikin harabar kamfanin ne da misalin ƙarfe uku na asuba.

Harin na daren Alhamis na zuwa ne shekara 10 bayan harin bom da aka kai wa ofisoshin kamfanin na This Day da ke Abuja da Kaduna.

Bayan shigar maharan cikin harabar kamfanin da ke unguwar Utako a birnin Abuja ne suka tara ma’aikatan a wuri guda, suna barazanar kashe su idan suka kuskura suka sanar da jami’an tsaro.

Arise News ta ambato jami’an tsaron da ke aiki a kamfanin suna cewa kafin tafiyar maharan, sun yi ƙoƙarin cewa za su sake dowawa.