An gudanar da taron tunawa da Marigayi Jiang Zemin

Daga CMG HAUSA

Da safiyar yau Talata ne aka gudanar da taron tunawa da marigayi Jiang Zemin, wanda ya rasu yana da shekaru 96 a ranar 30 watan Nuwamban da ya gabata.

An dai gudanar da taron ne a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing.

Kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin taron.

Tun a farkon taron, daukacin mahalarta sun yi shiru na mintuna 3, domin nuna alhanin rasuwar marigayi Jiang. (Mai fassara:Saminu Alhassan)

Sanarwar kwamitin jana’izar Jiang Zemin ta uku

Bayan rasuwar Jiang zemin, shugabannin kasashe, da gwamnatoci, da majalissu, da hukumomin gwamnatoci, da jam’iyyu, da kungiyoyin kasa da kasa, da jakadun kasa da kasa dake kasar Sin, da aminan ketare dake rayuwa a kasar Sin, da Sinawa mazauna ketare, da ‘yan uwan dake rayuwa a yankunan Hong Kong, Macau, da Taiwan da dama sun aike da sakwannin ta’aziyya, tare kuma da halartar bukukuwan jimamin da aka shirya, a nan bari mu nuna muku babbar godiya.

Mai fassara: Jamila