Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama ƙunshi 28 na tabar wiwi a hannun wani mutum da ake zargi dillalin miyagun ƙwayoyi ne.
Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce an kama wanda ake zargin ne, Ibrahim Usman mai shekara 37, a wani samame na sirri da aka gudanar a kan hanyar Mashi zuwa Birnin Kuka, da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar 20 ga Yuli.
Ya ce binciken da jami’an suka yi ya gano ƙunshi 28 na busasshiyar ganyen da ake zargin tabar wiwi ce.
A cewar rundunar, wanda ake zargin ya amsa cewa yana safarar miyagun ƙwayoyin ne domin sayarwa a Jihar Katsina da sauran sassan ƙasar.
’Yan sanda sun ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da gargaɗin masu aikata irin waxannan laifuffuka da su daina ko kuma su fuskanci hukunci.
