An kashe mata biyu a cibiyar addinin Musulunci a Lisbon

‘Yan sanda sun ce wani mahari ya kashe wasu mata biyu, bayan da ya daɓa musu wuƙa a wata cibiyar addinin Musuluci a Birnin Lisbon na Ƙasar Portugal.

An kai harin ne a cibiyar addinin Musulunci ta ‘Ismaili Centre’ da ke birnin.

‘Yan sanda sun samu nasarar harbe maharin, wanda ke riqe da sharveviyar wuƙa a ƙafa, bayan da ya yi yunqurin guduwa.

Kawo yanzu dai ba a san dalilin maharin na kashe matan ba.

‘Yan sanda sun ce sun samu kiran waye inda aka shaida musu cewa, an ga maharin ya shiga cibiyar da misalin ƙarfe 11 na safe agogon ƙasar.

Shugaban cibiyar Nazim Ahmad, ya ce, maharin ɗan Afghanista ne, yayin su kuma matan biyu ‘yan Portugal ne.

A wata sanarwar da cibiyar addinin ta fitar a shafinta na intanet, ta ce, ta kaɗu matuƙa da kisan matan, tare da alƙawarta bayar da tallafi ga iyalan mamatan.