An yi murnar bikin kunna fitilu na Yuanxiao a sassa daban-daban na ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA

A ƙarshen lokacin hutu na murnar Bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar ƙasar Sin, an yi murnar bikin kunna fitilu na Yuanxiao a sassa daban-daban na ƙasar, inda aka ji daɗin kallon fitilu masu siffofi daban-daban, da gasar kacici kacici da ɗanɗana abincin Yuanxiao, a ƙoƙarin bayyana kyakkyawan fatan mutane kan zaman rayuwa mai daɗi.

A bikin nune-nunen fitilu a wurin shan iska na gwada lambuna na Zhengzhou dake lardin Henan, fasahar zamani ta haskaka wata al’adar gargajiyar Sinawa wato kallon fitilu. Fitilu masu siffofi daban-daban waɗanda aka ƙera bisa fasahohin zamani sun haskaka duhun dare, sun kuma sanya bikin kunna fitilu na Yuanxiao ya amsa sunansa sosai.

Ban da haka kuma, a jajibirin bikin na Yuanxiao, an yi gasar kacici-kacici domin murnar bikin a birnin Tongling na lardin Anhui, inda mutane masu tarin yawa suka halarta. Ke Zi’ang, wani mazauni birnin ya ce, “Gasar kacici kacici a bikin Yuanxiao ya taimaka min ƙara fahimtar basirar al’ummar Sinawa da ma al’adunmu mai dogon tarihi. A gani na, murnar wannan biki ta hanyar gargajiya yana da matuƙar ban sha’awa.”