Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Fitaccen ɗan siyasa daga Jihar Kano na Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya mai suna Dan Bilki ya sha tsabga a jikinsa cikin wani bidiyo wanda ya mamaye yanar gizo a ranar Alhamis ɗin nan, inda wasu waɗanda ba a gama sanin ko su waye ba suka zane shi tsaf bisa zargin sa da cin zarafin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani.
Tun da farko an ji mutane su na umartar Ɗan Bilki, wanda ke cikin ankwa, da ya gabatar da kansa, inda kuma ya yi hakan, sannan suka tuhume shi da dalilinsa na sukar gwamnan, duk da cewa, shi ba ɗan asalin jihar ta Kaduna ba ne, inda nan take ya ƙaryata hakan cikin rawar jiki.
Ɗan Bilki dai ya yi shuhura wajen tsoma baki kan harkokin siyasar Nijeriya a shirye-shiryen gidajen rediyo da kafafen sadarwa na zamani.An yayin da ake tsula ma sa bulalar bayan an nemi ya durƙusa, an ji Kwamamda ya na cewa ya na fama da ciwuka, ciki har da na zuciya.
A wani bidiyon kuma sai aka nuno Kwamanda yana zargin Gwamna Sani da aiko mutanensa,don su doke shi.Ya ce, Gwamna Uba Sani ne ya turo su kuma zai iya gane wasu daga cikinsu da inda suka samo ankwar da suka ɗaure shi da ita, ya na mai cewa, wasu ’yan sanda ne suka aikata masa hakan su na masu barazanar za su kashe shi.
Sai dai kuma, a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kaduna, Muhammad Lawal Shehu, ta ce, ta bayar da umarnin a gudanar da bincike kan bidiyon.A cewar sanarwar, “an janyo hankalin Gwamnatin Jihar Kaduna kan wani bidiyo da ya yaɗu mai ɗauke da wani Ɗan Bilki Kwamanda, wanda wasu mutane da ba a san ko su waye ba su na azabtar da shi.
“A cikin bidiyon, an zargi Gwamnatin Jihar Kaduna.
To, Gwamnatin Jihar Kaduna ta na mai matuƙar nesanta kanta da wannan ɗanyen aiki. Hakan ba ya cikin ɗabi’armu. Babu irin wannan taɓargaza a cikin al’ummarmu.
“Mun yarda da doka da bin ƙa’idoji. Gwamnatinmu ta adalci ce, daidaito, tafiya da kowa da girmama mutuntakar ɗan adam. tun kafa Gwamnatin Jihar Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Sanata Uba Sani mu ke aiki tuƙuru wajen ganin mun tabbatar da aminci tare da jan dukkan ’yan ƙasa a jika.
“Mu na amsar dukkan ra’ayoyi da bayar da kyakkyawan yanayin siyasa ga kowa. Gwamnan Jihar Kaduna ya daɗe kan tafarkin yaƙi da tauye haƙƙin bil adama da ’yanci. Bai taɓa yin baya-baya ba wajen tabbatar da kare ’yan ƙasa, bin doka da ƙa’ida ba. Ba kuma zai taɓa yarda a cikin kowane irin yanayi ya bayar da ƙofar azartar da wani, don kawai saɓanin ra’ayi ba.
“Don haka Mai Girma Gwamna Uba Sani ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin. A ci alwashin bin diddigin lamarin tun daga tushe, don ganowa da tabbatar da cewa, doka ta yi aikin ta kan waɗanda suka aikata ta’asar.”
