Ana sa ran Cop15 zai kai ga wani sabon matsayi bayan yarjejeniyar Paris

Daga CMG HAUSA

Idan an ce yarjejeniyar Paris ta samar da muhimmin ci gaba a fannin tinkarar sauyin yanayi, yanzu haka kuma ana sa ran taron COP15 da ake gudanarwa, zai kai ga wani sabon matsayi kamar wannan yarjejeniya.

A daren jiya Alhamis 15 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron manyan shugabanni a mataki na biyu na taron COP15 da aka yi a birnin Montreal na kasar Canada ta kafar bidiyo.

A cikin jawabin da ya yi, shugaba Xi ya yi kira ga daukacin al’ummar duniya da su yi hadin kai wajen ingiza samun bunkasuwa, tare da kiyaye muhalli, da ma kafa kyakkyawar makomar duniya ta bai daya, da samar da wata duniya mai tsabta. Xi ya kuma ya gabatar da shawarwari guda 4 game da wannan buri, da mataki da kuma kokarin da Sin ke yi a matsayin kasa mai shugabancin COP15, don ingiza kiyaye mabambantan hallitu a duniya.

Mai fassara: Amina Xu