Ana tattauna yiwuwar yafe wa Nijeriya da ƙasashen Afirka bashi – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Daidai lokacin da saura shekara ɗaya mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙare, wanda a tsawon shekaru bakwai da ya shafe ya fi kowa ciwo wa ƙasar nan bashi, shugaban ya bayyana cewa tattaunawar yiwuwar yafe wa ƙasashen Afirka bashi na kan hanya.

Ya ce manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe na duniya na tattauna yiwuwar yafe wa ƙasashen Afirka bashin dala biliyan 650.

Buhari wanda ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, ya bayyana haka ne a wurin buɗe taron kwanaki uku na Taron Kakakin Majalisun Tarayyar Ƙasashen Afirka da aka buɗe ranar Litinin a Abuja.

Kusan tun bayan hawan Buhari mulki Nijeriya ta bazama ta na ciwo bashi a ƙasashe daban-daban domin yin ayyukan raya ƙasa. Wannan lamari kuwa a kullum sai ƙara janyo wa mulkin sa baƙin jini yake yi.

Buhari ya ce ya zame wa ƙasashen Afirka tilas su ciwo bashin domin yin wasu manyan ayyuka.

Ya ce Nijeriya ta ciwo biliyoyin daloli bashi, waɗanda suka ƙara haifar wa ƙasar wawakeken giɓi.

Shugaban Bankin Bunƙasa Afirka AfDB, Akinwumi Adesina, ya yi jawabi inda ya ce tattalin arzikin Afrika ya samu koma baya da kashi 1.5 sanadiyyar ɓarkewar Korona a duniya.