APC a Zamfara ta caccaki EFCC kan zargin Matawalle da karkatar da N70bn

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta nuna damuwarta bisa zargin da hukumar EFCC ta yi na cewa Gwamnan jihar, Hon. Bello Mohammed Matawalle, ya karkatar da kimanin Naira biliyan 70 a lokacin mulkinsa.

Tare da cewar zargin ya biyo bayan kiran da Matawalle ya yi ga hukumar ta EFCC da ta binciki wasu mutane a Fadar Shugaban Ƙasa da kuma wasu daga cikin ministocin gwamnatin Buhari.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Yusuf Idris, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin, ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan rahoton hukumar ta yaƙi da cin hanci da rashawa na karkatar da Naira biliyan 70 da gwamnatin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ta yi.

Jam’iyyar ta bayyana zargin hukumar EFCC a matsayin cin mutunchin Gwamna Bello Matawalle, tare da da bayyana cewar zargin ba shi da tushe balle makama.

“Ya kamata hukumar ta EFCC ta fara da binciken yawan adadin kuɗin da Jihar Zamfara ta samu a cikin shekaru huɗu da suka gabata, albashin ma’aikatanta na wata-wata, ayyukan cigaban da aka samar a ƙarƙashin gwamnatin Matawalle ciki har da ƙoƙarinsa na magance matsalar tsaro, ayyukansa a fannin kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa na zamantakewa,” in Jam’iyyar.

Ta ƙara da cewa, “Ba shakka kuma babu mamaki hukumar EFCC ƙarƙashin Abdurrashid Bawa ta yi ta ƙoƙarin gano dalilan da za ta ɓata wa Gwamnan Zamfara suna, kuma a lokacin da abun ya gagara sai ta yi ƙoƙarin neman cin hanci daga gurinsa.

“Yayin da wannan ma ya ci tura, sai hukumar ta fake da irin kiraye-kirayen da Gwamnan ya yi na a binciken mutanen da ke cikin gwamnatin Buhari mai barin gado, waɗanda suka ɓata sunan Shugaban Ƙasa, hakan ya sa EFCC ta bayyana wannan zargin ta bakin shugabanta da masu daukar nauyinsu”. Sanarwar ta karanta.

“A matsayinmu na ‘yan Najeriya muna da ‘yancin sanin matakin da Mista Bawa zai dauka game da wannan batu, mu kuma yi kira da a kafa kwamitin bincike kan Bawa wanda shi ma ya kamata ya fito ya kare kanshi bisa yadda ya jagorancin hukumar.

“Za mu ci gaba da jira kuma muna da yakinin cewa ko da gwamnatin Buhari ba ta yi haka ba don rashin lokaci, shugaba mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu zai yi.”