Editor

9513 Posts
Raɗɗa ya rantsar da kwamishinoni da mashawartansa

Raɗɗa ya rantsar da kwamishinoni da mashawartansa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya rantsar da kwamishinoni da masu ba shi shawara ta musamman su 38 da za su kasance 'yan majalisar zartarwar jihar. A bikin rantsuwar da ya gudana a filin taro na 'Peoples' Square, Katsina, an rantsar da kwamishinoni 20 da masu ba Gwamna shawara ta musamman su 18. A jawabin gwamna Raɗɗa ya hori waɗanda aka rantsar ɗin da su sani cewa amana ce aka damƙa musu, don haka suke da buƙatar su tsare ta kamar yadda Allah Ya buƙata. Gwamnan ya tabbatar musu da cewa ba zai…
Read More
Marubuta tamkar madubi muke ga al’umma – Zainab Sarauniyar Kanawa

Marubuta tamkar madubi muke ga al’umma – Zainab Sarauniyar Kanawa

"Wasu makaranta su ne ciwon kan marubuci" Daga ADAMU YUSUF INDABO Fitacciyar matashiyar marubuciya littafan adabin Hausa da ke cin kasuwar su a yanar gizo, wato Zainab Salihu Yarima da aka fi sani da 'Sarauniyar Kanawa' faɗi haka ne a yayin da take yin kira ga takwarorinta marubuta da su ji tsoron Allah su zama masu tsaftace alƙalumansu, don rubuta abun da zai zama mai amfanarwa ga al'umma bakiɗaya, wanda bai ci karo da addini da kuma al'adar Malam Bahaushe ba. Marubuciya Zainab Salihu Yarima (Sarauniyar Kanawa) dai ta yi wannan kira ne a yayin tattaunawarta da wakilinmu Adamu Yusuf…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: APC ta zaɓi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyya na ƙasa

Da Ɗumi-ɗumi: APC ta zaɓi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyya na ƙasa

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Shugabanni na Ƙasa (NEC) na Jam'iyyar APC, ta zaɓi tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa. Kazalika, jam'iyyar ta zaɓi tsohon mai magana davyawun Shugaban Majalisar Dattawa, Ajibola Basiru, a matsayin sakatarenta na ƙasa. Kwamitin (NEC) ya yi wannan zaɓen ne yayin zamansa karo na 12 da ya gudanar ranar Alhamis Transcorp Hilton da ke Abuja. Mahalarta taron sun haɗa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, gwamnonin APC da sauransu. Sai dai, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo na daga cikin…
Read More
Zan Kammala aikin hanyar Wuju-wuju kafin kwana 100 a ofis – Gwamna Abba

Zan Kammala aikin hanyar Wuju-wuju kafin kwana 100 a ofis – Gwamna Abba

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya ba da tabbacin zai kammala aikin hanyar Wuju-wuju mai nisan kilomita 1.2 kafin ya cika kwana 100 a ofis. Yusuf ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar gani da ido game da yadda aikin hanyar ke gudana. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a Kano a ranar Laraba. Dawakin-Tofa ya rawaito Gwamnan na cewa, an ba da kwangilar aikin hanyar ne a lokacin wa'adin mulki na biyu na tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso. Gwamnam ya ce, “Burina ya…
Read More
Cire tallafin fetur: Gwamnatin Zamfara za ta raba kayan abinci

Cire tallafin fetur: Gwamnatin Zamfara za ta raba kayan abinci

Daga WAKILINMU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada umurnin gaggauta raba kayan abinci a ƙananan hukumomi 14 da ke faɗin Jihar domin rage raɗaɗin wahalar da janye tallafin fetur ya jefa al'umma. Wata sanarwa wacce mai magana da yawun gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa za a yi rabon kayan abinci ne duba da irin mawuyacin halin da al'umma ke ciki, kuma bisa ƙudurin gwamnatin Jihar na bin duk wata hanya ta sauƙaƙa wa jama'a. Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta yi shiri mai kyau don tabbatar da cewa mabuƙata sun amfana da wannan…
Read More
NLC ta dakatar da ƙudirin tafiya yajin aiki – Fadar Shugaban Ƙasa

NLC ta dakatar da ƙudirin tafiya yajin aiki – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da ta 'yan Kasuwa (TUC) sun amice da su dakatar da ci gaba zanga-zangar da suka fara. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Mista Dele Alake, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a Abuja. Ya ce an cim ma hakan ne biyo bayan tattauna da ƙungiyoyin suka yi da Shugaba Tinubu inda suka nuna gamsuwarsu dangane da tabbacin da Shugaban ya ba su na cim ma buƙatunsu. Yayin tattaunawar, Comrade Joe Ajaero ne ya jagoranci ɓangaren NLC, yayin da Comrade Festus Usifo ya…
Read More
Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen ministoci 19 da Tinubu ya aika wa Majalisar Tarayya

Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen ministoci 19 da Tinubu ya aika wa Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana sunayen ministoci kashi na biyu da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aika wa Majalisar domin tantacewa. A ranar Labara Shugaba Tinubu ya tura wa Majalisar ta Dattawa da ƙarin sunaye 19 ta hannun Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila. Sunayen da Tinubun ta tura wa Majalisar sun haɗa da tsaffin gwamnoni Bello Matawalle (Zamfara), Atiku Bagudu (Kebbi), Simon Lalong (Plateau), Ibrahim Geidam (Yobe) da kuma Isiaka Oyetola (Osun). Sauran su ne, Abdullahi Gwarzo, Bosun Tijani, Maryam Shetty, Isiak Salako, Tunji Alausa, Yusuf Sunusi, Ibrahim Geidam, Lola John, Shuaibu Audu,…
Read More
Ruwan sama mafi ƙarfi cikin shekaru 140 ya haifar da mummunar ambaliya a ƙasar Sin

Ruwan sama mafi ƙarfi cikin shekaru 140 ya haifar da mummunar ambaliya a ƙasar Sin

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Chana sun ce, an samu ambaliya mai ƙarfi a wasu sassan ƙasar, musamman a yankunan Mentougou da Fangshan da ke birnin Beijing na kasar, sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a yankunan da lamarin ya shafa. An ce ambaliyar ta yi sanadiyyar lalata matsugunnan al'ummar yankin da dama, ta kuma haifar da zaizayar ƙasa. Ɗan jarida daga ƙasar, Murtala Zhang, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba cewa, "…mamakon ruwan sama da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi, wanda ba a taɓa ganin irin ƙarfinsa ba a shekaru 140 da…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya miƙa wa Majalisa sunayen ministoci kashi na biyu

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya miƙa wa Majalisa sunayen ministoci kashi na biyu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya miƙa wa Majalisar Tarayya sunayen ministocinsa kashi na biyu don tantancewa. Tinubu ya miƙa sunayen ne ta hannun Shugaban Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila a ranar Laraba. Manhaja ta tattaro cewar sunayen sun shafi jihohin Adamawa, Bayelsa, Gombe, Kano, Kebbi, Kogi, Lagos, Plateau, Osun, Yobe da kuma Zamfara. Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis ta makon jiya Gbajabiamila ya miƙa kashin farko sunayen mutum 28 ga Majalisar Dattawa domin tantace su a matsayin ministoci. Ƙarin bayani na tafe…..
Read More
Masu zanga-zanga sun karɓe harabar Majalisar Tarayya

Masu zanga-zanga sun karɓe harabar Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Mambobin ƙungiyar ƙwadago da ke gudanar da zanga-zanga a Abuja sun karɓe harabar Majalisar Tarayya a ci gaba da zanga-zangar tasu da suka fara a ranar Laraba. Majiyarmu ta ce masu zanga-zangar sun karɓe harabar majalisar ne jim kaɗan bayan da sanatoci suka shiga ganawar sirri. Ta ƙara da cewa, sun samu shiga harabar Majalisar ne bayan da suka ɓalle babbar get ta ɗaya da ta biyu na shiga harabar. NLC da dangoginta sun fara zanga-zanga ne domin nuna adawarsu dangane da matsin rayuwar da suka ce gwamnati ta jefa 'yan ƙasa ciki sakamakon cire tallafin mai.…
Read More