Editor

9513 Posts
Zanga-zanga: Mataimakin Gwamnan Neja ya yi wa NLC mubaya’a

Zanga-zanga: Mataimakin Gwamnan Neja ya yi wa NLC mubaya’a

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Comrade Yakubu Garba, ya yi wa Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar mubaya'a game da zanga-zangar lumanar da ta fara gudanarwa a wannan Laraba. Da yake jawabi a wajen taron, Garba ya bai wa ƙungiyar muhimman shawarwari da kuma hanyoyi da ya kamata ta bi wajen ci gaba da gudanar da ayyukanta don amfanin al'umma baki ɗaya. Manhaja ta kalato cewar, Mataimakin Gwamnan shi ne shugaban ƙungiyar ƙwadago a jihar gabanin tsayar da shi takara a matsayin mataimakin gwamna. Majiyarmu ta ce jami'an da suka mara masa baya ciki har da Shugaban…
Read More
Yadda ake amfani da mata a yaƙin neman zaɓe, ba a cin moriyar da su ya sa na shiga siyasa- Fatima SBN

Yadda ake amfani da mata a yaƙin neman zaɓe, ba a cin moriyar da su ya sa na shiga siyasa- Fatima SBN

"Babban burina na ga matsalolin mata sun ragu ko da ba su tafi gabaɗaya ba" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Hajiya Fatima Suleiman Baban Nana, na ɗaya daga cikin matasan ƴan siyasa mata a Jihar Gombe, wacce kuma take taka rawar gani wajen kare haƙƙoƙin mata da ba su tallafi don inganta rayuwarsu. Mace ce mai kishin ganin mata sun samu kulawa da gatan sa za su taimaki kansu da iyalinsu. A zantawar da ta yi da wakilin Manhaja Blueprint, Abba Abubakar Yakubu, ta bayyana masa gwagwarmayar da take yi ƙarƙashin ƙungiyarta ta OPWIN, da abin da ya zaburar da ita…
Read More
BIDIYO: Zanga-zangar NLC a Abuja

BIDIYO: Zanga-zangar NLC a Abuja

Daga BASHIR ISAH Kamar yadda ta sha alwashi, Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta fara gudanar da zanga-zangar a sassan ƙasa. A Babban Birnin Tarayya, Abuja, an ga mambobin ƙungiyar sun mamaye ƙofar shiga Babbar Kotun Tarayya da ke birnin. NLC ta bakin shugabanninta, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin nuna rajin jin daɗinta kan tsadar rayuwar da 'yan Nijeriya ke fuskanta a sakamakon cire tallafin mai. Don haka take buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da za su sanyaya wa 'yan ƙasar ƙuncin rayuwar da suke fuskanta haɗi da sauran buƙatun ƙungiyar. Kalli bidiyon cuncurundon da…
Read More
“Ya kamata a bar talaka ya numfasa”

“Ya kamata a bar talaka ya numfasa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wani bidiyo da ake yaɗawa ta kafafen sada zumunta, an nuna Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin wani jawabi da ya yi cikin harshen Turanci, a lokacin yaqin neman zaɓe yana ambata cewa, ya kamata a bar talaka ya numfasa! A lokacin shi ma da kansa ya nuna tausayawa ga halin da talakan ƙasar nan ke ciki, don haka yake kwaɗaitarwa 'yan Nijeriya cewa, a ƙarƙashin gwamnatinsa za a samu walwalar rayuwa, har a dara. Kuma a kan haka talakawan ƙasar nan mafiya rinjaye suka zaɓe shi, bisa tunanin idan ya hau mulkin ƙasar nan…
Read More
An cafke masu ƙoƙarin kitsa juyin mulki a Sierra Leone

An cafke masu ƙoƙarin kitsa juyin mulki a Sierra Leone

Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a ƙasar Sierra Leonean sun ce sun tsare mutane da dama, ciki har da jami'an soji waɗanda ke shirin kai harin tada zaune tsaye a ƙasar. Wannan na zuwa ne shekara guda bayan mummunan rikicin da ya auku a ƙasar a watan Agustan 2022, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30. 'Yan sandan sun ce “Ɓangaren tsaron ƙasar na bibiyar bayanan sirri dangane da ayyukan wasu ɗaiɗaikun 'yan ƙasar, ciki har da sojoji waɗanda suke ƙoƙarin daburta zaman lafiya a ƙasar. Jami'an sun ƙara da cewa, waɗanda ake zargin sun shirya yin amfani da…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a Legas

Da Ɗumi-ɗumi: Jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a Legas

Wani jirgin sama mai saukar ungulu da ba a kai ga tantancewa ba ya yi hatsari a yankin Oba Akran Ikeja a Jihar Legas. An ce jirgin ya faɗa wani gini ne kana daga bisani ya kama da wuta a wannan Talatar. Majiyarmu ta ce an samu ceto mutum huɗu da ke cikin jirgin da ransu in ji wani jami'in hukumar NEMA. Ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga gano dalilin aukuwar hatsarin ba.
Read More
Jarumi Kanayo O. Kanayo ya gargaɗi masu fim kan yadda suke yaudara ta hotuna da kwalliya a finafinansu

Jarumi Kanayo O. Kanayo ya gargaɗi masu fim kan yadda suke yaudara ta hotuna da kwalliya a finafinansu

Daga AISHA ASAS Shahararren ɗan wasan fim a masana’antar Kudu, wato Nollywood ya gargaɗi masu shirya finafinai kan yadda suke bayyana ababen da ke voye gaskiyar rayuwa ta mutanenmu, ta hanyar amfani da aiki daban da abinda yake zahiri, tare kuma da kwaikwayon ababen da suka bambanta da ababen da muka sani, wanda hakan ke kai masu kallo ga ruɗani kan wanene daidai, tsakanin gaskiya da kuma abinda ake nunawa, yayin da ta wani vangaren zai iya zama silar rashin tagomashin finafinan, dalilin gyara da mai kallo zai ta cin mai shiryawa. Jarumin ya yi wannan kira ne a ranar…
Read More
Duk mai son kawo ɓarna a Kannywood ya kama gabansa, don yanzu lokacin gyara ne, inji Abba El-Mustapha

Duk mai son kawo ɓarna a Kannywood ya kama gabansa, don yanzu lokacin gyara ne, inji Abba El-Mustapha

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Sabon Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab'i ta Jihar Kano ya sha alwashin duk mai yiwuwa wajen kawo gyara da kyautata ɗabi'un jama'a a matsayin sa na shugaban hukumar iya tsawon lokacin da Allah ya ba shi dama zai yi a kujerar shugabancin nasa. Abba El-Mustapha ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 24 ga Yuli, a lokacin da yake jawabi a gaban ɗumbun jama'a na cikin masana'antar Kannywood da kuma masoyansa da suka raka shi ofishinsa domin kama aiki. Abba El-Mustapha ya fara da cewa, "Ni ɗan fim ne da ke taka rawa da…
Read More
Ana mallakar zuciyar namiji ta hanyar naci?

Ana mallakar zuciyar namiji ta hanyar naci?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da haɗuwa a wani sabon makon a shafin zamantakewa na jaridarki mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu tattauna a kan yadda wasu matan kan yi naci su bibiyi namiji don samun cimma buƙatarsu ta mallakar zuciyar namijin da suke so. Kodayake dai Hausawa sun ce, wai namiji zomo ne wai ba a kama shi daga zaune. Ma'ana, namiji sai an dage ake samun sa a hannu. Haka kuma sun ce, yau da gobe ba ta bar komai ba. Wataƙila wannan ta sa wasu matan suke ƙarfafa nacinsu a kan namiji…
Read More
Shin za mu iya kawar da furfura bayan ta fara fitowa?

Shin za mu iya kawar da furfura bayan ta fara fitowa?

Daga AISHA ASAS Sananniyar magana ba a iya kawar da ci gaban fitowar furfura bayan ta fara fitowa, a nan ina nufin hanata fitar ba wai rufe ta da kala bayan ta fito ba. A lokacin da masu haƙƙin samar da baƙin gashi na jikin ɗan Adam suka tsayu kan fitar da farin gashin, to fa muddin suka fara, ba kuma abin da za ka yi da za su saurare ka, har su dawo ma da launinsu na farko. Kaso mafi rinjaye na masana sun tafi kan sai dai ka yi kwaskwarima a waje bayan ta fito ta hanyar sanya…
Read More