Shin za mu iya kawar da furfura bayan ta fara fitowa?

Daga AISHA ASAS

Sananniyar magana ba a iya kawar da ci gaban fitowar furfura bayan ta fara fitowa, a nan ina nufin hanata fitar ba wai rufe ta da kala bayan ta fito ba.

A lokacin da masu haƙƙin samar da baƙin gashi na jikin ɗan Adam suka tsayu kan fitar da farin gashin, to fa muddin suka fara, ba kuma abin da za ka yi da za su saurare ka, har su dawo ma da launinsu na farko.

Kaso mafi rinjaye na masana sun tafi kan sai dai ka yi kwaskwarima a waje bayan ta fito ta hanyar sanya lalle ko kuma ababen ture furfura, wato dyeing a Turance, amma ba wani magani da ka iya kawar da ita.

Shi ya sa masana suka fassara ta da sananniyar al’ada ta jikin ɗan adam. Wannan ga furfurar da ta fito bisa lokaci, wato gangarar shekaru.

A ɓangaren furfura da ta fito ta sanadiyar cuta, damuwa, rashin sinadarin bitamin ko ƙarancin abinci mai gina jiki, a nan an samu saɓani, wasu na ganin idan har aka samu waraka daga musababin fitowarta, za a iya samun fitowar sabon gashin mai ɗauke da launin baƙi.

Duk da cewa su ma sun amince bai zama dole hakan ta kasance ba. Yayin da wani ɓangaren na masana suka ce sam ba dawowa daga duniyar furfura, idan an tafi, an tafi kenan.