Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A shekara ta 1839, an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma ɗan tireda daga Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amurka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo ƙarshen cinikin bayi a Amurka.
Babu dai takamaimen lokacin da ake iya cewa shi ne lokaci da aka haifi Sengbe Pieh, sai dai masana tarihi sun yi ittifakin cewa, an haife shi ne a shekarar 1814 a ƙasar da a yanzu ake kira Saliyo.
An yi imanin an haife shi a wani tsibiri da ke gundumar Bonthe, wajen da ya yi ƙaurin suna wajen kiwon kifi. Pieh na shirin zama babban manomin shinkafa kuma a lokacin da aka sace shi, yana da mata da ’ya’yansa biyu mata biyu da namiji guda.
Mutane da dama a ganin Pieh ya fito ne daga ƙabilar Mende, mafi girma ke nan a ƙasar Saliyo, wasu masana tarihi na musanta hakan, inda suke cewa ɗan ƙabilar Shebro ne. Tsibirin Bonthe wanda har ila yau ake kira tsibirin Shebro, wuri ne da al’ummar Shebron ke zaune a ciki a ƙasar ta Saliyo.
Daga baya ne mutanen Mende suka zauna a wajen. Saboda auratayya da aka samu tsakanin dumbin mazauna wajen, galibin ’yan Shebro kan ɗauki kansu a matsayin ’yan ƙabilar Mende. Baki ɗayansu dai sun saje ta yadda da wuya ka iya bambance tsakanin ɗan asalin Mende da kuma Shebro a Saliyo.
Cikin watan Janairun 1839, yayin da ya ke manomin shinkafa, Sengbe Pieh ya shiga hannu kuma aka sayar da shi ga masu sayen bayi ’yan asalin ƙasar Spain, a wani waje da ake kira Sulima na kudancin ƙasar Saliyo. An tasa ƙeyar Pieh tare da wasu bayi da dama daga Saliyo ta ƙarfin tsiya zuwa birnin Havana na ƙasar Kuba inda aka je aka yi gwanjonsu.
Yayin da iyayen gidan Pieh da sauran bayin ke tafiya da su zuwa gonaki, cikin jirgin ruwa da ake kira La Amistad, Sengbe Peih ya lallava ya tsinka marin da aka ɗaure shi da shi, sai kuma suka kwashi wuƙaƙen da aka ajiye don sare rake, daga nan sai tawaye ya tabbata. Sun kashe matuƙin jirgin da mai dafa abinci suka kuma tilasta wanda ya saye su juya akalar jirgin don ya koma Saliyo.
Amma ta hanyar amfani da wasu dabaru, aka yaudari Pieh da sauran ‘yan Afirka manyan da ƙananan da ke jirgin, cikin dare ya yi ta sauya hanya ya doshi ƙasar Kuba. Sai dai wata iska mai ƙarfi daga bisani ta karkata jirgin zuwa gaɓar ruwan Amurka. Daga nan kuma aka kama Pieh da abokan tafiyarsa aka garƙame su bisa tuhumar kisan kai da kuma fashin kan teku.
Sai dai wata ƙungiyar da ke yaƙi da cinikin bayi wadda daga bisani ta amsa sunan ‘The Amistad Committee’ ta yi nasarar ƙalubalantar shari’ar kuma a ƙarshe aka sake su, koda ya ke an samu wasu ma daga cikin ‘yan Afirka da suka rasa rayukansu a lokacin da suka fafata a kan hanyar.
Bayan ƙungiyar ‘Amistad Committee’ ta haɗa isassun kuɗaɗe, an mayar da Pieh da sauran ‘yan Afirka tare da wasu Kiristoci ‘yan Mission zuwa Saliyo a watan Janairun shekara ta 1842.
Lallai labarin Sengbe Pieh shi ne tushen gangamin yaƙi da cinikin bayi a Amurka. Babu wani littafin cinikin bayi a Amurkar da zai kasance cikakke ba tare da ya ƙunshi kukan kura ko bajintar da Sengbe Pieh ya yi ba.
Ana koyar da tarihin Pieh a wasu jami’o’i da kuma kafa mutum-mutuminsa a wasu jihohin Amurka. Kamfanin haɗa fina-finai na Hollywood ma ya shirya wani fim da ya nuno tarihin wannan jarumin mutum. Komawar Pieh ƙasarsa ta Saliyo ma ta buɗe ƙofa ga Kiristoci masu aiki Mission.
Sengbe Pieh ya mutu ne a shekarar 1879. Babu cikakkun bayanai kan ko ya sake haɗuwa da iyalinsa ko kuma akasin haka. An yi imanin cewa an binne shi ne a wani wajen bauta da ke Bonthe. Shi dai Pieh wani jarumi ne daga cikin al’ummar Poro wadda ke da alaƙa da ’yan ƙungiyar asiri.
Don haka ne gano asalin kabarinsa ke da wuya saboda sai an bi wasu hanyoyi na tsafi. A yanzu ma’aikatar kula da harkokin yawon shaƙatawa na cewa za ta sake tono Sengbe Pieh don sake binne shi a wani wajen da mutane ke iya zuwa don kallon kabarinsa.
Sengbe Pieh, mutum ne da ya yi imanin cewa babu wani bambanci tsakanin ɗan Adam, ma’ana babu bambanci na launin fata ko wajen da mutum ya fito. Ya yi yaƙin ƙwato wa kansa ‘yanci da ma sauran wasu da aka sanya bisa tafarkin da ya tsinki kansa na cinikin bayi.
Akwai hotonsa a kan takardar kuɗin ƙasar Saliyo. A baya-bayan an sanya wa wata babbar gada da ke birnin Freetown sunansa. Ana kuma iya ganin hotunansa a wurare da dama a birnin na Freetown fadar gwamnatin ƙasar Saliyo.