Zanga-zangar gamagari: Babu gudu ba ja da baya, cewar NLC

Daga BASHIR ISAH

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce babu gudu ba ja da baya dangane da zanga-zangar da ta ƙudiri aniyar gudanarwa kan cire tallafin mai.

Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ne ya shaida wa manema labarai hakan jim kaɗan bayan kammala taro da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan rage raɗaɗin cire tallai mai da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ya ce shirinsu na ma’aikata su shiga zanga-zangar lumana ya zuwa ranar Laraba na nan bai canza ba.

Ajaero ya ƙara da cewa, yana da yaƙinin ɓatagari ba za su yi amfani da wannan dama wajen cutar da al’umma ba, ya ce haƙƙi ne a kan jami’an tsaro su bai wa ma’aikatan kariya a yayin zanga-zangar.

Haka nan, shugaban na NLC ya bayyana shakkunsa kan ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai iya magance matsalar hauhawar farashin kayayyakin da ake fuskanta a ƙasa.

Ya ce an ɗage ci gaba da tattaunawar tasu zuwa ranar Talata domin bai wa shugabannin NLC zarafin sauraren jawabin Shugaba Ƙasa da ya gabatar ranar Litinin.