Ana mallakar zuciyar namiji ta hanyar naci?

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da haɗuwa a wani sabon makon a shafin zamantakewa na jaridarki mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu tattauna a kan yadda wasu matan kan yi naci su bibiyi namiji don samun cimma buƙatarsu ta mallakar zuciyar namijin da suke so.

Kodayake dai Hausawa sun ce, wai namiji zomo ne wai ba a kama shi daga zaune. Ma’ana, namiji sai an dage ake samun sa a hannu. Haka kuma sun ce, yau da gobe ba ta bar komai ba. Wataƙila wannan ta sa wasu matan suke ƙarfafa nacinsu a kan namiji har suke ganin za su iya kai wa ga biyan buƙatarsu ta mallakar zuciyarsa ko samunsa a hannu.

Akwai wasu lokuta da mace da kanta za ta ga namijin da take so, amma saboda kunya ta ‘ya mace, sai ta kasa iya furta tana sonsa, wata ma tana iya furtawa ɗin amma wani lokacin cikin rashin sa’a, sai a qi karvar soyayyar tata.

Wata kuma suna tsaka da soyayya kawai sai ya fara baya-baya da ke. Ya sauya mata. Ya daina amsa wayarki ko saƙonninki, kuma shi ma sam ya daina kira ko amsa saƙonki. Bar ta batun zuwa gidanku tuni ma ya ɗauke ƙafa kamar an yi ruwa an ɗauke. Wannan shi ma yana sa mace ta shiga damuwa. Wasu sukan rabu da mazan, shikenan. Wasu kuma sukan cigaba da kafiya da naci.

Wani lokacin kuma ma aure aka yi. Amma sai miji ya kasance cikin halin ko-in-kula da mace. Wani da ma can haka ɗabi’arsa take, wani kuma bayan auren ya canza. To shi ma wasu matan suna ‘yan dabaru wasu kuma sai su ɗauki ɓaragen kafiya da naci don samun shawo kansa.

Akwai dalilai da yawa da ke sa namiji ya ƙi amsa soyayyar macen da ta fara sonsa. Bisa ɗabi’a ta namiji ya fi sabawa ya ga mace yana so, ba wai a ce ana sonsa ba. Maza ɗaiɗaiku ne kawai suke na’am da soyayya idan mace ta ce tana sonsu. Haka wani namijin yana ɗaukar macen da ta fara nuna tana sonsa a matsayin ba ta kai ba. Ko ba ta da aji.

Shi wani namiji ya ɗauka duk wata mace mai ƙima da mutunci jiravtake a so ta. Haka wasu matan yanayin halittarsu yadda suke ko ɗabi’arsu wataƙila bai dace da irin matar da yake so ba, ko kuma ma yana da wata budurwar daban. Ko kuma ma a tsarinsa iyaye yake so su zavar masa mata ba ya son ya zava da kansa. Dalilai da yawa dai za su iya sa namiji ya ji bai son macen da ta ce ko ta nuna tana sonsu.

Wasu mazan kuma sai suna tsaka da soyayya da mace sai ka ga sun fara janye jiki. Wani janye jikin ba don ba ya son ki ba ne, ko don zai rabu da ke ba ne. Kawai shi namiji bayan ya gama bibiyar mace don ta ce tana sonsa, idan har ya samu wannan biyan buƙatar ta samun zuciyarta kuma ko ya aure ta, sai ya samu kwanciyar hankali. Saboda kawai yanzu ya aminta kin kamu da son shi.

To yanayin ɗabi’arki gare shi a wannna al’amari zai sa ya cigaba da tafiya da ke ko akasin haka. Wani kuma da gaske ja bayan so yake ya rabu da ke ɗin! Wataqila ya qyalla ya hango wata, ko kuma ya yi istihara ya ga ba alkhairi a tarayyar, ko kuma ya fuskanci ɗabi’unki ba su dace da irin matar da yake so ya aura ba, sai ya dinga janye jiki. Wataran ma shikenan sai ya rabu da ke. Wani kuma mayaudari ne, zuwa ya yi don yin lalata da ke. Da zarar ya samu biyan buƙata, shi ma sai ya ƙara mai.

Wasu matan daga sun ga haka, za su amshi ƙaddara su ƙara gaba. Amma wata ba za ta iya haƙura ba, sai ta yi naci ta ga abinda ya ture wa buzu naɗi. Ba komai ba sai saboda dalilai da dama kamar haka:

*So: So dai kamar yadda muka sani makaho ne, ba ruwansa da ana sonka ko ba a sonka. Kamar amai yake ko haɓo. Idan suka yunƙura sai sun taho. Kuma mace ba ta iya haƙura da wanda ta fara so duniya, sai dai idan faɗan ya fi ƙarfinta. Haka wani ma ba soyayyar farko ba ce, amma haka idan son ya sarƙafe ta sai ta yi ta wahalar bibiyar wanda take so. Kuma sai ta ga idan ba shi ɗin ba, duk duniya ma ba za ta taɓa ganin wanda take so ba.

*Son yin aure kawai ma yana sa mace ta yi ta nace wa namiji ko da ba ta ra’ayinsa in dai tana ganin kamar za ta samu karɓuwa, ko shi ne take ganin zai iya aurenta a cikin manemanta, sai ta yi ta naci. Wata ganin ta daɗe a ƙasa ba miiji, ga qawayenta duk sun yi aure kawai so take ita ma ta yi ta huta. Kuma wataƙila ba wasu manema gare ta ba.

*Kwaɗayi: Wasu matan kwaɗayi na sakawa su yi wa namiji naci saboda kuɗinsa ko kyawunsa.

Ɗabi’a: Wata macen kuma ɗabi’arta ce haka, duk abinda take so, ba ta son ta rasa. Ta fi son kullum ta zama mai galaba a abubuwanta. Shi ma idan tana ganin namiji zai kufce mata, ko ta halin ƙaƙa sai ta kafa naci son ta same shi.

Kishi da isa: Wata tana ganin idan ta bar ka kamar wata za ka je ka so. Kishin wannan ke sa ta nace.

Ɓata lokaci: Wata za ta ga ta ɓata lokaci mai yawa a kanka ko ta yi asara har da ta dukiya. Za ta ga kawai idankuka rabu ta yi asarar duk waɗannan.

Jiran tsammani: Wata kuma tana jiran ka zuwa wani lokaci da take ganin za ka iya aurenta.

Waɗannan wasu dalilai ne manya da suke sa mata su yi wa namiji naci don su mallake shi. Amma ba nacin aka ce kada a yi ba, amma rabon mutum ba ya wuce shi. Indai shi ne mijin aurenki ba zai wuce ki ba. Kuma shi nacin nan, duk da watarana akan haɗu da biyan buƙata.

Illolin naci a soyayya

Naci yana sa a lalata yarinya. Wata idan ta kafa wa namiji naci har ya gane cewa ita ke sonsa foye da nasa, yakan yi amfani da damar don bautar da ita ko don lalata ta don ya san a lokacin burinta kada ya guje ta.

Duk nacin yarinya a kan namiji da gudun ɓacin ransa indai ba don Allah ba ne, wallahi sai ya gudu ɗin dai da take tsoro. Daga ya samu buƙatarsa shikenan.

Naci ko ya yi ƙarko daga ba ya ba ya ɗorewa. Namiji ya fi daraja abinda ya sha wahala ya nema ya samu.

Don haka, Idan mace ta lura namiji ya janyep daga gareta, kada ta matsa, ko ta makale mashi. Ta nemi dalili, idan bai fada ba ta kyale shi. Idan bai dawo ba shi ba nata bane.

Naci a kan so, yana ragekimarki. Ko kasuwa idan mutum ya sayi abu da tsada ya fi daraja shi a kan wanda ya samu da arha. Ki zama mai tsada sai a daraja ki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *