Editor

9513 Posts
Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A shekara ta 1839, an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma ɗan tireda daga Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amurka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo ƙarshen cinikin bayi a Amurka. Babu dai takamaimen lokacin da ake iya cewa shi ne lokaci da aka haifi Sengbe Pieh, sai dai masana tarihi sun yi ittifakin cewa, an haife shi ne a shekarar 1814 a ƙasar da a yanzu ake kira Saliyo. An yi imanin an haife shi a wani tsibiri da ke gundumar Bonthe, wajen da ya yi ƙaurin…
Read More
Zanga-zangar gamagari: Babu gudu ba ja da baya, cewar NLC

Zanga-zangar gamagari: Babu gudu ba ja da baya, cewar NLC

Daga BASHIR ISAH Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce babu gudu ba ja da baya dangane da zanga-zangar da ta ƙudiri aniyar gudanarwa kan cire tallafin mai. Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ne ya shaida wa manema labarai hakan jim kaɗan bayan kammala taro da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan rage raɗaɗin cire tallai mai da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ya ce shirinsu na ma'aikata su shiga zanga-zangar lumana ya zuwa ranar Laraba na nan bai canza ba. Ajaero ya ƙara da cewa, yana da yaƙinin ɓatagari ba za su yi…
Read More
Ina duba yiwuwar ƙarin albashin ma’aikata – Tinubu

Ina duba yiwuwar ƙarin albashin ma’aikata – Tinubu

Daga WAKILINMU Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya bayyana cewa nazarin yiwuwar yi wa ma'aikata ƙarin albashi. Ya bayana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasa da yammacin ranar Litinin. Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ɗauki tsauraran matakai ne saboda sun zama dole, “kuma babu waɗanda suka fi su sauƙi.” Ya ce, “Da a ce akwai hanyoyin da suka fi su sauƙi da na bi. “Abin da zan iya yi kawai shi ne ɗaukar matakan da za su sauƙaƙa yanayin. “Gwamnatina za ta tabbatar da yin aiki tare da dukkan jihohi don rage raɗaɗin da…
Read More
Gidauniya ta bai wa Hajiyar da ta maido da tsintuwar N84m tallafin N250,000

Gidauniya ta bai wa Hajiyar da ta maido da tsintuwar N84m tallafin N250,000

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gidauniyar TY Buratai Humanitarian Foundation da ke da shelkwata a Jihar Nasarawa, ta bayar da gudunmawar Naira 250,000 ga Mahajjaciyar jihar Zamfara, Hajiya Aisha Muhammad Yanguru Nuhuche, wadda ta tsinci Dala 80,000 kwatankwacin sama da Naira miliyan 84 sannan ta maida kuɗin ga mahukunta a ƙasa mai tsarki. Gidauniyar ta kuma karrama ta da takardar shaidar karramawa a matsayin Jakadiyar Gaskiya. A nasa jawabin shugaban gidauniyar, Hon. Ibrahim Dahiru Ɗanfulani a hedikwatar hukumar alhazai ta jihar Zamfara da ke Gusau, ya bayyana cewa, abin da Hajiya A’isha ta yi ta cancanci yabo. Ya ce, an…
Read More
Kano: Za a kammala titin Wuju-wuju, Kasuwar Kwankwaso nan ba da daɗewa ba – Kwamishina

Kano: Za a kammala titin Wuju-wuju, Kasuwar Kwankwaso nan ba da daɗewa ba – Kwamishina

Daga RABIU SANUSI a Kano Kwamishinan Ma'aikatar Bibiyar Ayyuka da Nazari na Jihar Kano, Hon Ibrahim Namadi Dala, ya tabbatar da yunƙurin gwamnati Jihar Kano wajen ƙarasa ayyukan da ta sa gaba na Titin Wuju-Wuju da Kasuwar Zamani dake Garin Kwankwaso a Ƙaramar Hukumar Madobi da ma wasu ayyukan. Ibrahim Namadi ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar Laraba yayin da ya fita rangadin duba ayyukan da ba a kammala ba da aka fara tun lokacin Dr Rabiu Musa Kwankwaso da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta yi watsi da su. Namadi ya ce, babu abun bacin rai da ya…
Read More
Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi a yau

Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi a yau

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai yi wa 'yan ƙasa jawabi da misalin ƙarfi 07:00 na dare yau Litinin. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta bakin mai bai wa Tinubu shawara kan ayyuka na musamman da harkokin sadarwa, Dele Alake. Sanarwar ta ce ana buƙatar gidajen talabijin da rediyo da sauransu, da su jona da Tashar Talabijin ta Ƙasa da kuma Tashar Rediyo ta ƙasa don yaɗa jawabin Shugaba Ƙasar kai tsaye. Sai dai sanarwar ba ta fayyace dalilin da ya sa Tinubun zai yi 'yan ƙasa jawabin ba.
Read More
Harin ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutum 44 a Pakistan

Harin ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutum 44 a Pakistan

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Pakistan sun ce, aƙalla mutum 44 mutu sannan sama da 100 sun jikkata a wani mummunan hari da aka kai wajen wani taron siyasa a ƙasar. Jami'an yankin sun ce, sun gano wasu abubuwa da ke tabbatar da cewar harin na ƙunar-baƙin-wake ne. Harin ya auku ne a Arewa maso Yammacin gundumar Bajaur kuma a daidai lokacin da mambobin jam'iyyar Jamiat Ulema-e-Islam-Fazl (JUI-F) ke tsaka da taro. Bayanai sun ce, an kammala aikin ceto a wurin da aka kai harin bayan da jami'ai suka samu nasarar kwashe dukkan waɗanda suka jikkata zuwa aisibiti. Sai…
Read More
Dandalin shawara: Ki taimaka min da bayani kan ‘khul’i’

Dandalin shawara: Ki taimaka min da bayani kan ‘khul’i’

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. An wuni lafiya, ya aiki. Wata baiwar Allah ce ta ke neman shawara. Mijina ba mutumin arziki ba ne, ya kasance mai yawan musgunawa iyalinshi, ba ci, ba sha, bare sutura ga kuma neman mata, wallahi ko ɓoyo na ganin ido ba ya yi min. An kai shekara uku rabon da ya ba ni kuɗi wai da sunan cefane a ci abinci a gidansa. Komai ni nake yi wa 'ya'yana, har makaranta ma da taimakon wata baiwar Allah mai bada tallafi ta sa su, ni sai na ji da kuɗin tafiyarsu da abinci. Ni…
Read More
Yajin aiki: Ba mu yarda da ƙarin albashin 25% ba – Likitoci

Yajin aiki: Ba mu yarda da ƙarin albashin 25% ba – Likitoci

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NARD) ta ƙi amincewa da ƙarin kashi 25 na albashi da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi don inganta albashin likitoci. Ƙungiyar ta ɗauki matakin ƙin amincewar ne a wajen taron shugabanninta na ƙasa (NEC) da ya gudana a Legas, inda ta fitar da bayanin sakamakon taro a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Orji Emeka Innocent da sakatarenta na ƙasa, Chikezie Kelechi da kuma Umar Musa. Likitocin sun dage kan cimma ainihin buƙatunsu da suka haɗa da cikakken aiwatar da tsarin albashi na CMSS da aka amince…
Read More
Tsohuwar matar sarki ta maka Sarkin Dutse, Hamim Sanusi a kotu kan batun gado

Tsohuwar matar sarki ta maka Sarkin Dutse, Hamim Sanusi a kotu kan batun gado

Daga WAKILINMU Tsohuwar matar Sarkin Dutse, Hajiya Asiya Nuhu Sanusi, ta maka Sarkin Dutse, Ahaji Hamim Nuhu Sanusi, a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a kan abin da ya shafi gado. Asiya tare da wasu mutum bakwai sun maka Sarki Hamim Nuhu Sanusi da wasu mutum shida a kotu ne inda suke ƙalubalantar hukuncin da Kotun Upper Shari’a 1, ƙarƙashin jagorancin Khadi Ado Birnin Kudu ta yanke kan batun gadonsu. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar, ƙarar wadda suka shigar ta hannun Barista Abdulhali Ali Esq, ta haɗa da Kotun Upper Shari’a 1 inda a nan aka fara shigar da…
Read More