04
Aug
*An kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su Daga BASHIR ISAH Dakarun haɗin gwiwa na rundunar Hadarin Daji mai aikinta a jihohin Sakkwato, Katsina, Kebbi da Zamfara sun fatattaki 'yan bindiga a maɓuyarsu da ke shiyyar Arewa maso Yamma tare da kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su. Kazalika, sojoji sun ƙwace wasu kayayyaki daga 'yan bindigar yayin samamen da suka haɗa da bindigogi da alburusai da babura da shanu da sauransu. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Hedikwatar tsaro ta fitar a ranar Juma'a. Sanarwar ta ce a ranar 3 ga Agusta, sojoji…
