Editor

9513 Posts
Daƙile matsalar mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Daƙile matsalar mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Matsalar mace-macen mata da yara a lokacin ciki ko haihuwa dai ta jima ta na ci wa ƙasashe masu tasowa tuwo a ƙwarya. Alal misali, ƙasashen da suka ci gaba mata 7 zuwa 15 ne ke mutuwa a cikin mata masu juna 100,000 daga lalurar ciki ko haihuwa; amma a ƙasashe masu tasowa har wajen mata 100-300 ne kan rasu sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa. Wani sabon rahoton da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar na cewa a duk minti biyu mace na mutuwa a duniya yayin da take ɗauke da juna biyu ko haihuwa. Hakan na ƙara nuna rashin…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta rufe iyakar Nijeriya da Nijar

Gwamnatin Tarayya ta rufe iyakar Nijeriya da Nijar

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da rufe iyakar Nijeriya da Nijar da ke Katsina, lamarin na zuwa ne duba da halin rashin tabbas da ake ciki a ƙasar Nijar tun bayan da sojojin ƙasar suka kifar da gwamnatin dimokaraɗiyya a ƙasar. Muƙaddashin shugaban hukumar fasa ƙwauri, Bashir Adewale ne ya sanar da rufe iyakokin ƙasashen biyu. A ziyarar da ya kai don tabbatar da ana bin dokar rufe iyakokin da ke Jibiya a jihar Katsina, shugaban hukumar ya bayyana cewar rufe iyakokin muradun dukkan ƙasashen biyu ne. Ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya ta…
Read More
Amfani da ƙarfin soji a Nijar ba daidai ne ba – Majalisar Malamai

Amfani da ƙarfin soji a Nijar ba daidai ne ba – Majalisar Malamai

Daga BASHIR ISAH Zauren Majalisar Malamai ta Ƙasa reshen Kano ya nuna damuwarsa kan gargaɗin da ƙungiyar ECOWAS ta yi wa waɗanda suka yi juyin mulkin a ƙasar Nijar. Zauren ya bayyana damuwar tasa ne yayin taron da ya gudanar a ranar Juma'a. Cikin sanarwar bayan taro da zauren ya fitar, bayan nazari da lura da ya yi, ya kums ba da shawarari da yake ganin za su taimaka wajen samun maslaha a Nijar ba tare da amfani da ƙarfin soji ba. Zauren ya ba da shawarar cewar, "Gwamnatin Nijeriya da kuma ECOWAS su bar wannan hanya da ta saɓa…
Read More
Sama da ɗalibai 23,000 suka amfana da tallafin karatu na gwamnatin Jihar Nasarawa – Sa’adatu Yahya

Sama da ɗalibai 23,000 suka amfana da tallafin karatu na gwamnatin Jihar Nasarawa – Sa’adatu Yahya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Babbar Sakatariyar Hukumar Samar da Tallafin Karatu ta gwamnatin Jihar Nasarawa, wato Nasarawa State Scholarship Board a turance, Hajiya Sa’adatu Yahya ta ce kawo yanzu gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta bada tallafin karatu wa sama da ɗalibai ‘yan asalin jihar dubu 23 don ba su damar cigaba da karatunsu a manyan makarantun jihohin da ƙasa baki ɗaya. Hajiya Sa’adatu Yahya ta sanar da haka ne a lokacin da take tattaunawa da wakilin mu a ofishin ta dake hukumar a garin Lafiya babban birnin jihar ranar Talata 1 ga watan Yulin shekarar 2023 da ake…
Read More
Tsadar rayuwa: Kafa dokar taɓaci a rayuwar mu gabaɗaya ita ce mafita, cewar jama’ar Gombe

Tsadar rayuwa: Kafa dokar taɓaci a rayuwar mu gabaɗaya ita ce mafita, cewar jama’ar Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Rayuwa a Nijeriya a yau ta kai intaha, yunwa da talauci sun kama gida a duk faɗin ƙasar, sun zama tsumagun cikin gidaje, ba ma na kan hanya ba, musamman gidajen marasa galihu. Daga Gabas da Yamma, zuwa Kudu da kuma Arewa, batun duk ɗaya ne. Wasu a garin Gombe, kuka suke yi gwamnatin jihohi su bubbufe rumbunan abinci su yi ta raba wa al’umma. Waɗansu kuma kira suke yi da Gwamnatin Tarayya da ta tallafa wa talakawa da “maƙudan kuɗaɗe” ta asusun bankunan su. Sai dai kuma a nashi martanin, wani Injiniya wanda kuma…
Read More
FIFA za ta biya kuɗin fafatawa a kofin duniya ga asusun ’yan wasa kai tsaye

FIFA za ta biya kuɗin fafatawa a kofin duniya ga asusun ’yan wasa kai tsaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Ƙwallon Ƙafar Duniya (FIFA) ta sanar da aniyarta ta biyan kuɗaɗen da ake bai wa duk tawagar da aka dama da ita a gasar kofin duniya ta Australia da New Zeland kai tsaye ga asusun ajiyar ’yan wasan maimakon ta biya hukumar ƙwallon ƙafar ƙasashensu. Ta shafi tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya, Super Falcons. Tun da farko an jiyo kocin tawagar Falcons ɗin, Randy Waldrum yana cewa akwai wasu ’yan wasan tawagar da har yanzu suke bin haƙƙoƙinsu tsawon shekaru biyu. Wannan lamari dai ya janyo tada jijiyoyin wuya, inda har ya kusan yin…
Read More
Sanatocin Arewa sun gargaɗi ECOWAS kan amfani da ƙarfin soji a Nijar

Sanatocin Arewa sun gargaɗi ECOWAS kan amfani da ƙarfin soji a Nijar

Daga BASHIR ISAH Sanatocin Arewa sun gargaɗi Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan aiki da ƙarfin soji wajen maido da dimokuraɗiyya a Jamhuriyar Nijar. Sanatocin ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdul Ahmad Ningi (Bauchi), sun ce amfani da tsarin diflomasiyya ne mafita wajen dawo da gwamnatin dimokraɗiyya a ƙasar ta Nijar. Cikin sanarwar da sanatocin suka fitar ta bakin kakakinsu, Suleiman A. Kawu Sumaila, sun yi gargaɗin amfani da ƙarfin soji zai haifar da asarar rayuka a ƙasar Nijar da maƙwabtanta. Sanarwar ta ce, “Ba mu yarda da amfani da ƙarfin soji…
Read More
An kashe ’yan ta’adda 36, an kama 137, an ceto mutum 140 – Hedkwatar Tsaro

An kashe ’yan ta’adda 36, an kama 137, an ceto mutum 140 – Hedkwatar Tsaro

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) a ranar Alhamis ta ce, sojojin da aka tura sassa daban-daban na ƙasar sun kashe ’yan ta'adda 36, sun kuma kama ’yan bindiga 137 da kuma mara musu baya 6. Rundunar sojin ta kuma ce, sojojin sun kama mutane 15 da suka yi satar mai tare da kwato kuɗi Naura 3,177,650.00 tare da kuɓutar da mutum 140 da aka yi garkuwa da su. Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya kuma bayyana cewa, an ƙwato…
Read More
Mai Shari’a Rabi Umar ta nuna damuwa game da yawaitar matasa a gidajen yari a Bauchi

Mai Shari’a Rabi Umar ta nuna damuwa game da yawaitar matasa a gidajen yari a Bauchi

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi A ƙoƙarinta na ganin ta inganta ayyukan shari'a tare da rage cunkoso a gidajen yari, babbar Mai Sharia ta Jihar Bauchi Hajiya Rabi Talatu Umar ta fara rangadin gidajen gyaran tarbiyya na Jihar Bauchi don gane wa idonta yadda alƙalai ke gudanar da ayyukansu tare kuma da duba yiwuwar rage cunkoso a gidajen yari. Ziyarar da ta fara a ranar Litinin ta ziyarci Darazo da Misau da Gamawa da Zaki da Azare da Ningi yadda a gidan gyaran tarbiyya na Gamawa ta ga matasa sama da 100 suna jiran shari'a. Don haka ta nuna rashin…
Read More
Za mu farfaɗo da yawon buɗe ido da bunƙasa al’adun mu a Kano – Tukur Sagagi

Za mu farfaɗo da yawon buɗe ido da bunƙasa al’adun mu a Kano – Tukur Sagagi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Manajan Darakta na hukumar yawon buɗe idanu na Jihar Kano Hon. Tukur Bala Sagagi ya bayyana cewa damar da ya samu na kula da hukumar da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba shi ya ji daɗi, dama ce da zai taimaka wa al'umma, yarda da ƙauna ce tasa aka kira shi aka ce ya zo ya yi. Ya ce abin dai kuma abin rashin daɗi shi ne yadda suka taras da abubuwa sun lalace sun ragargaje ba ɗa'a, ba ƙima ba tsafta, ba kayan aiki a hukumar. Ya ce abin mamaki kwamfuta wannan…
Read More