Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da rufe iyakar Nijeriya da Nijar da ke Katsina, lamarin na zuwa ne duba da halin rashin tabbas da ake ciki a ƙasar Nijar tun bayan da sojojin ƙasar suka kifar da gwamnatin dimokaraɗiyya a ƙasar.
Muƙaddashin shugaban hukumar fasa ƙwauri, Bashir Adewale ne ya sanar da rufe iyakokin ƙasashen biyu.
A ziyarar da ya kai don tabbatar da ana bin dokar rufe iyakokin da ke Jibiya a jihar Katsina, shugaban hukumar ya bayyana cewar rufe iyakokin muradun dukkan ƙasashen biyu ne.
Ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya ta umarci masu ruwa da tsaki a sha’anin iyakokin da su tabbatar ana bin umarnin rufe iyakokin da suka haɗa ƙashen biyu.
“Shugaba Tinubu shi ne zakaran gwajin dafi na inganta tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma.
“Ya yi amannar cinikayya tsakanin ƙasashe maƙota zai kawo wa ‘yan Nijeriya cigaban arziƙi da ma wasu sauran mutanen yankin.
“Ya nuna hakan a baki da kuma aikace, mai yiwuwa hakan ne ya taimaka masa wajen zama shugaban ƙungiyar ƙasashen tattalin arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS, wata guda da kama aiki a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya.
“To, yanzu mun shiga wani yanayi na rashin tabbas da rashin tsaro.
“Wannan yanayi ba zai bayar da damar gudanar da kasuwanci ba Cikin sauƙi.
“Babu ta yadda za mu iya gudanar da harkokin kasuwanci cikin kwanciyar hankali kamar yadda ake gani a jamhuriyar Nijar.”
Ya ci gaba da cewa, wannan shi ne dalilin da ya sa shugabannin ECOWAS suka zartar da hukuncin rufe dukkan iyakokin Nijeriya da suka haɗa da Nijar.
A cewarsa, alhakin hukumar fasa ƙwauri ta Nijeriya ne da sauran hukumomin tsaro na gwamnati su aiwatar da umarnin.