Editor

9513 Posts
Mun riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 saboda maguɗin jarrabawa – WAEC

Mun riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 saboda maguɗin jarrabawa – WAEC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Shirya Jarrawaba ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta saki sakamakon jarrabawar kammala sakandare na 2023 a ranar Litinin. Da yake jawabi shugaban WAEC a Nijeriya, Patrick Areghan, ya ce daga adadin ɗalibai 1,613,733 da suka rubuta jarrabawar an riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 bisa dalilai masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Ya ce an samu ci gaba dangane da ƙaruwar samun nasara a jarrabawar, inda ɗalibai 1,361,608 kwatankwacin kashi 84.38 cikin 100 na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar suka samu makin 'credit' da sama da haka wanda ya haɗa da darussan Ingilishi da Lissafi ko babu. Sai kuma…
Read More
’Yan damfara na karɓar bashin banki da lambar wayar ’yan sanda

’Yan damfara na karɓar bashin banki da lambar wayar ’yan sanda

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya gargaɗi ’yan Nijeriya da su daina amfani da lambobin gaggawa na ’yan sanda wajen karɓar bashi daga bankuna da sauran kamfanonin ba da bashi. Egbetokun ya yi wannan gargaɗin ne ta wata sanarwa da kwamishinan ’yan sanda a babban birnin tarayya (FCT), CP Haruna G. Garba ya fitar a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli, 2023. Ya bayyana cewa, wasu mutane na amfani da layukan gaggawa cin bashin kamfanonin ba da bashi da ruwa. “CP ta umurci mutanen da ke shigar da layukan gaggawa na ’yan sanda a cikin mugayen ayyukansu,…
Read More
Dandalin shawara: Ki taimaka min da bayani kan ‘khul’i’ (2)

Dandalin shawara: Ki taimaka min da bayani kan ‘khul’i’ (2)

Tare Da AISHA ASAS Assalamu alaikum. An wuni lafiya, ya aiki. Wata baiwar Allah ce ta ke neman shawara. Mijina ba mutumin arziki ba ne, ya kasance mai yawan musgunawa iyalinshi, ba ci, ba sha, bare sutura ga kuma neman mata, wallahi ko ɓoyo na ganin ido ba ya yi min. An kai shekara uku rabon da ya ba ni kuɗi wai da sunan cefane a ci abinci a gidansa. Komai ni nake yi wa ‘ya’yana, har makaranta ma da taimakon wata baiwar Allah mai bada tallafi ta sa su, ni sai na ji da kuɗin tafiyarsu da abinci. Ni…
Read More
Rawar da kankana ke takawa a gyaran fata

Rawar da kankana ke takawa a gyaran fata

Daga AISHA ASAS Kankana na ɗaya daga cikin 'ya'yan itace da ke da matuƙar tasiri a gyaran fata da kuma kawar da cututtukan fata masu dama. Tana ɗauke da sinadaran da ke gusar da maiƙon da ke fita a hanyoyin fitar gumi, wanda idan ya yawaita zai iya haifar da fesowar ƙananan ƙuraje. Kankana na taka muhimmiyar rawa wajen gyara fatar da ta ke yawan yankwanewa, idan aka markaɗe ta (ba tare da an zuba mata ruwa ko kaɗan ba, kuma za a haɗe ne har 'ya'anta) aka zuba mata zuma kaɗan, ana shafawa a inda matsalar ta ke sau…
Read More
Manufarmu ce tsamo matasa daga ƙangin talauci da aikata laifuffuka – Kwamaret Alkamatu

Manufarmu ce tsamo matasa daga ƙangin talauci da aikata laifuffuka – Kwamaret Alkamatu

Kamfanin Alkamatu Kamfani ne da ya yi fice a jahar Kano, wajen samar wa da al'umma mafita don dogaro da kai. Sannan suna samar wa da mutane bashi daga bankuna tare da tallafin kuɗaɗe don cigaba da kasuwanci don tsayawa da ƙafafunsu. Wakilin Blueprint Manhaja a Kano, Babangida S. Gora ya samu tattaunawa da Shugaban Kamfanin Alkamawa. Ga yadda tattaunawar ta kasance.  MANHAJA: Da farko za mu so mu ji da wa muke tare. ALKAMATU: Ni Sunana Alkamatu Hussaini Abdulƙadir, Kuma ni ne shugaban wannan kamfani na Alkamatu BrainBox Solutions. Mene ne manufarka ta samar da wannan kamfani? to kusan…
Read More
Shigar Nijeriya hidimar yaƙi a Nijar: A yi hattara ko a sha kunya

Shigar Nijeriya hidimar yaƙi a Nijar: A yi hattara ko a sha kunya

Bayanan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke Yi da Nijeriya da ECOWAS na shirin kai hari wa sojojin Nijar, babbar kasada ce kowa ya iya allonsa ya wanke su ji da matsalar Zamfara da matsalar yunwa da boren da talakawa ke shirin shiga. Sun fi kowa sanin ba a raina yaƙi su tambayi Rasha a Ukraine yadda wanki ya Kai su dare kowane gefe ke asarar soja da dukiya. Sojojin Nijar ba kanwar lasa bane idan suka yi wannan kuskure kafin su kai Maradi ko Tahwa kan hanyar zuwa Niamey karon ba zai musu daɗi ba. Saboda na shiga Nijar…
Read More
Malagi ya zamo minista

Malagi ya zamo minista

An ce mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha roman sa. Ga dukkan alamu gwamnati shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu GCFR ta na son kafa kyakkyawan tarihi na gina gwamnati da kwararru ta fuskoki da dama. Jihar Neja za ta yi ministoci maau kwarewa kuma fitattu ta fuskar gogewa domin ɗauko Muhammed Idris Malagi a yi masa minista, wanda hakan wata manuniya ce a kan yadda shugaba Tinubu ke da tunani da ƙoƙarin janyo duk wanda ya cen centa. Ba zan ida wannan rubutu ba har sai na yaba ma ɗauko mutane kamar Act Musa Dangiwa da Hannatu…
Read More
Ina da ƙwarin gwiwar wata rana mijina zai dawo – Matar Dadiyata

Ina da ƙwarin gwiwar wata rana mijina zai dawo – Matar Dadiyata

Daga MAHDI M. MUH’D Khadija Ahmed Lame, uwargidan fitaccen marubuci a dandalin sada zumunta, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, ta bayyana fatanta na cewa maigidanta zai dawo gida wata rana. Ranar Laraba, 2 ga watan Agusta ake cika shekara huɗu da ɓatan Abubakar Idris, shahararre kuma marubuci a shafukan sada zumunta. A watan Agustan 2019 ne aka bi shi har gida a daidai lokacin da ya dawo daga tafiya, inda aka sace shi da motarsa. Tun sace shi da aka yi daga gidansa ba a sake jin labarinsa ba. Tun daga lokacin wasu suka zargi hukumar tsaron…
Read More
Shin lauyoyi ne kaɗai su ka yi fushi da sake kama Emefile?

Shin lauyoyi ne kaɗai su ka yi fushi da sake kama Emefile?

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Zan fara da batun Godwin Emefiele kafin shiga batun tsadar rayuwa. Haƙiƙa a ’yan kwanaki biyun nan labarun yadda ta kaya a kotun Legas kan dakataccen gwamnan babbban banki Godwin Emefiele ya zama kan gaba a kafafe. Ba kotu kaɗai ce ta buƙaci ko umurci ’yan sandan farin kaya DSS ssu sake Emefiele ko su gurfanar da shi gaban kotu. DSS ta cimma umurnin kotun don maimakon ta sake Emefiele ta zaɓi gurfanar da shi gaban kotu ne don fara cajin da da dalilan kama shi fiye da wata ɗaya da ya wuce. Rundunar farin…
Read More
Ƙarfafa ɓangaren kasuwanci ne mafita ga samar da aiki a Nijeriya – Malagi

Ƙarfafa ɓangaren kasuwanci ne mafita ga samar da aiki a Nijeriya – Malagi

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa ingantaccen fannin kasuwanci zai taimaka gaya wajen samar da guraben aiki a Nijeriya. Ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun ministocin Shugaba Bola Tinubu kuma mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja. Malagi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa don tantancewa a matsayin minista. Da yake jawabi, Malagi ya shawarci Hukumar Kula da Gidajen Talabijin da Rediyo ta Ƙasa (NBC) da ta bi diddigin lasisin gudanarwar da aka bai wa masu son kafa gidajen yaɗa labarai a faɗin ƙasa. Game…
Read More