Malagi ya zamo minista

An ce mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha roman sa. Ga dukkan alamu gwamnati shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu GCFR ta na son kafa kyakkyawan tarihi na gina gwamnati da kwararru ta fuskoki da dama.

Jihar Neja za ta yi ministoci maau kwarewa kuma fitattu ta fuskar gogewa domin ɗauko Muhammed Idris Malagi a yi masa minista, wanda hakan wata manuniya ce a kan yadda shugaba Tinubu ke da tunani da ƙoƙarin janyo duk wanda ya cen centa.

Ba zan ida wannan rubutu ba har sai na yaba ma ɗauko mutane kamar Act Musa Dangiwa da Hannatu Musa Musawa a jihar mu Katsina da cewa Tinubu ya yi tinani mai kyau. Haka a lamarin jihar Jigawa inda shi ma Badaru ya samu dama.

Sai kuma jagaba ta fuskar gwagwarmayar sai an yi Tinubu wato Malam Nasir Ahmed El-Rufai ɗauko shi Tinubu ya kyauta. A yankin kudanci dauko Barista Nyeson Wike a jihar Ribas da kuma dauko Devid Omahi a jihar Ebonyi duka alamu ne ma su fito da za ai gwamnati mai kyau. Allah ka jishe mu alkhairi.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519/08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *