Mun riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 saboda maguɗin jarrabawa – WAEC

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Shirya Jarrawaba ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta saki sakamakon jarrabawar kammala sakandare na 2023 a ranar Litinin.

Da yake jawabi shugaban WAEC a Nijeriya, Patrick Areghan, ya ce daga adadin ɗalibai 1,613,733 da suka rubuta jarrabawar an riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 bisa dalilai masu nasaba da maguɗin jarrabawa.

Ya ce an samu ci gaba dangane da ƙaruwar samun nasara a jarrabawar, inda ɗalibai 1,361,608 kwatankwacin kashi 84.38 cikin 100 na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar suka samu makin ‘credit’ da sama da haka wanda ya haɗa da darussan Ingilishi da Lissafi ko babu.

Sai kuma ɗalibai 1,287,920 kwatankwacin 79.81 na jimillar ɗaliban, sun samu makin ‘credit’ da sama da haka da yaɗa da darussan Lissafi da Ingilishi.