Majalisa ta tabbatar da Malagi a matsayin Minista

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dattawa ta tabbatar da mawallafin Jaridun Blueprint da Manhaja, Mohammed Idris Malagi daga Jihar Neja a matsayin Minista a Gwamnatin Bola Tinubu.

Wannan na zuwa ne bayan shafi kimanin mako guda da Majalisar Dattawa ta yi tana tantance sunayen da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike mata don naɗa su muƙaman ministoci.

Daga cikin waɗanda suka bi sawun Malagi wajen tabbatar da su a matsayin minista har da Dele Alake (Ekiti), tsohon Gwamnan Jihar Ribas Governor Nyesom Wike da tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Festus Keyamo, SAN, da sauransu.

Malagi, Alake da Wike na daga cikin kashin farko na sunaye 28 da Shugaba Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa a ranar Alhamis ta makon jiya inda aka tantance su a ranar Larabar da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *