Dandalin shawara: Ki taimaka min da bayani kan ‘khul’i’ (2)

Tare Da AISHA ASAS

Assalamu alaikum. An wuni lafiya, ya aiki. Wata baiwar Allah ce ta ke neman shawara. Mijina ba mutumin arziki ba ne, ya kasance mai yawan musgunawa iyalinshi, ba ci, ba sha, bare sutura ga kuma neman mata, wallahi ko ɓoyo na ganin ido ba ya yi min.

An kai shekara uku rabon da ya ba ni kuɗi wai da sunan cefane a ci abinci a gidansa. Komai ni nake yi wa ‘ya’yana, har makaranta ma da taimakon wata baiwar Allah mai bada tallafi ta sa su, ni sai na ji da kuɗin tafiyarsu da abinci.

Ni dai kam ba zan ce ma ki na san daɗin aure ba, amfani ɗaya aure ya yi min shi ne, samun ‘ya’ya, ko shi kuwa kawai Allah ya ƙaddaro ne, don sai mu yi wata shida bai neme ni ba, sai ran da ya bushi iska zai kusance ne, kuma da ya gama ba ruwansa da tawa buƙatar. Na yi kai ƙara, na yi roƙo, amma shiru ka ke ji.

Shi ne fa na kai maƙura, na nemi ya sawwaqe min ko na huta. To sai ya je ya ɗauko wani malami wai ya gaya min abinda Allah Ya ce idan mace ta nemi saki, shi ne fa ya kira wata kalma wai ita ‘khulu’i’, ya yi bayanin kan wai idan Ina son mijina ya sawwaƙe min, to zan ba shi kuɗin sadaki, kuɗin da zai yi hidimar biki, da kuɗin da zai kama hayar inda zai sa matar ko na shekara biyu ne.

Aka yi lissafin kuɗi zunzurutu har dubu ɗari uku da arba’in. Wai su ne kuɗin da zan biya in fitar da kaina daga zaluncin mijina. Kuɗin da ko a ido ban taɓa ganinsu ba.

Shi ne na ce bari na aiko da tambayata gare ki, duk da na san ba za ki tuna ni ba, amma Ina ɗaya daga cikin masoyanki da suka yi kiranki a shekarun baya su na gaishe ki. Don Allah Ina son ƙarin bayani kan wannan ‘khulu’i’ da suka ce, da kuma tambayar ko akwai wani sasauci da Musulunci ya yi wa irinmu marasa ƙarfi, waɗanda azaba ta sa su neman rabuwa ba son zuciya ba. A gaida yara. Na gode.

AMSA:

Menene hukuncin mace ta nemi khul’i?

Khul’i a Musulunci abu ne da ba a so a yi, wato makaruhi, sai dai akwai ta inda zai iya zama haramun ga mace. Idan mace ta nemi khul’i bisa wani ƙwaƙwaran dalili da idan ta ci gaba da zama da mijin zata iya cutuwa, ko zata iya sava masa, wanda zai kai ta ga fushin Allah, wannan shi ne khul’i da ba a so a yi ba, amma ya halasta a yi shi, don babu zunubi idan an aikata.

Idan kuwa mace haka kawai ta bushi isaka, ta ji kawai tana son rabuwa da mijinta, ba laifin tsaye ba na zaune, ba wani dalili, kawai tana kallon ƙyalƙyalin duniya, ko rayuwar rashin aure da sheɗan ke mata zuga kanta, to wannan shi ne khul’i haramtace, kamar hadisin Tirmizi, wanda Thawban ya ruwaito ya ce, manzon rahma ya ce, “matan da suka nemi mijinsu saki ko khul’i ba tare da wani dalili ba, suna daga cikin mata munafukai.”

Shin nawa ne kuɗin da mace zata fanshi kanta da su?

Malamai sun ɗan samu bambanci a ƙididige abinda miji zai amsa, kasantuwar lamarin na yarjejeniya, don haka wasu ke ganin ya danganta ne da yadda yarjejeniyar ta kasance. Wasu kuwa na kallon dalilin neman rabuwar, idan hujja ce ta aduba mata sai su yi ƙoƙarin kawo sasauci a ciki.
A wani ɓangare wasu malamai na fatawar cewa, sadakinsa ne zata mayar masa da shi kawai, wasu kuma na ganin har da ɗan abinda zai taimaka ya yi wani auren. Don haka za mu iya cewa ya danganta da inda aka kai lamarin da kuma hujjojin da aka bayar yayin yanke hukuncin.

Menene matsayarki a khul’i?

Idan har abinda ki ka faɗa gaskiya ne na mijinki ba ya ciyar da ke, ba ya baki wasu daga cikin haƙƙoƙin da mata take da su kan mijinta, kuma a bisa waɗannan dalilai ne ki ke son rabuwa da shi, to akwai magana biyu kan irin hukuncin da ya kamata a yi gare ki don samun sasauci.

Wasu malamai sun tsayu kan cewa, ba za ki ba wa mijinki ko ƙwandala ba, dalilin kuwa shi ne, Allah Maɗaukakin Sarki ya shar’anta wasu haƙƙoƙin da suka rataya kan mijinki da zaran ya aure ki, waɗanda aka ce tun kan ya yi aure ya kamata ya san da zamansu, idan har ba zai iya sauke su ba, to aure bai wajaba kansa ba.

Waɗannan haƙƙoƙin sun haɗa da ciyarwa, tufatarwa da kuma biya mata buƙata a yayin kwanciyar aure.

Idan namiji ba shi da halin iya kula da mace na daga ciyarwa ko tufatarwa, addinin Musulunci ya ce, ya yawaita azumi don rage wa kansa sha’awa, amma ba inda aka ce ya yi auren a haka. Anan kenan babu aure ga wanda bai iya ciyar da matar da zai aura.

Idan kuwa ba shi da lafiyar kusantar mace, nan ma ba a ce ya yi aure ba, don ba zai iya bata abinda yake haƙƙinta, idan ma bayan auren ne sai ya fahimci cewa, ba ya iya gamsar da ita a shimfiɗa, Musulunci ya ce, adalci ne ya sawwaƙe mata ta je ta auri wanda yake daidai da ita.

Da wannan ne malaman da suka ce ba zata bayar da komai ba suka kafa hujja, inda suka ce, kotun Musulunci ce zata kai ƙara ko wani makamancin ta, idan har an tabbatar alƙalin ne zai yi yadda ya kamata, ta hanyar warware auren ba tare da khul’i ba.

Magana ta biyu ita ce, za ta mayar masa da sadakin sa kawai, ba tare da ƙarin komai ba. Malaman da suke wannan ɓangaren sun kafa hujja da cewa, ita ce ta nemi sakin da kanta, don haka ya zama khul’i, wannan zai sa hukuncin ya zama irin nasa, sai dai nata bisa sauƙi.

Idan kin fahimci bayyanin sosai, za ki gane cewa, ba Inda addini ya ce, sai kin ba wa mijinki kuɗi mai yawa irin wanda ki ka ambata, wannan zai sanar da ke malamin da ya zayyano ma ki wannan lissafin ya saka son rai ne a ciki, matuƙar dai ya san da halin da ki ke ciki.

Shawara

Ki kai buƙatarki gaban kotun Musulunci, inda ki ke hasashen za a iya yi ma ki adalci, ko kuma idan akwai malami na ƙwarai da ki ka yarda da shi, kuma yake shiga sha’ani irin wannan, ta hakan ne za ki samu adalci kuma a yi hukunci irin wanda Allah Ya shar’anta.

Allah ne mafi sani.