“Wasu makaranta su ne ciwon kan marubuci”
Daga ADAMU YUSUF INDABO
Fitacciyar matashiyar marubuciya littafan adabin Hausa da ke cin kasuwar su a yanar gizo, wato Zainab Salihu Yarima da aka fi sani da ‘Sarauniyar Kanawa’ faɗi haka ne a yayin da take yin kira ga takwarorinta marubuta da su ji tsoron Allah su zama masu tsaftace alƙalumansu, don rubuta abun da zai zama mai amfanarwa ga al’umma bakiɗaya, wanda bai ci karo da addini da kuma al’adar Malam Bahaushe ba. Marubuciya Zainab Salihu Yarima (Sarauniyar Kanawa) dai ta yi wannan kira ne a yayin tattaunawarta da wakilinmu Adamu Yusuf Indabo. Ga dai yadda cikakkiyar tattaunawar tasu ta Kasance.
MANHAJA: Wacce ce Zeey Sarauniyar Kanawa?
ZAINAB YARIMA: Da farko dai sunana Zainab Salihu Yarima, wacce aka fi sani a media da duniyar rubutu kuma shi ne Zeey yar mutan Zazzau, ko Sarauniyar Kanawa. An haife ni a garin Zaria, na yi makarantan primary na a Saminaka da islamiya daga baya na dawo Zaria na yi secondry school ɗina, sannan na tafi Maqarfi na yi school of health, yanzu haka ina aiki a ‘Barau Dikko Teaching Hospital Kaduna.’
Taƙaitaccen tarihina ke nan. Amma shi laƙabina na ‘Sarauniyar Kanawa’ ya samo asali ne daga zauren ‘Majalisan Marubuta’ irin ana chat ɗin nan, kanawa kowa ya taso mun suna tsokana ta ina ramawa, ga shi ni kaɗai ce a lokacin bazazzagiya, sai na ce musu su bi ni a hankali fa, domin ni sarauniyar su ce. Aka dunga musu na ce ni daga yau ma sunana sarauniyar kanawa. Ai sai ma na canja group name ɗina zuwa Sarauniyar Kanawa. To tin daga wannan lokacun sunan ya bi ni.
To ta ya Zeey ta tsinci kanta tsamo-tsamo a duniyar rubutu?
To a gaskiya dai ni na kasance ma’abociyar karance karance tun ina ‘primary school’ da na fara iya Hausa nake karatun littafi irin su ‘Magana Jari Ce’, ‘Iliya Ɗan Mai Ƙarfi’, ‘Shehu Umar’ da dai sauran su, to bayan na shiga ‘secondry school’ ɗina sai na koma karatun littafan yaƙi har ta kai ta kawo ina samun littafi ina rubutawa. Idan na rubuta in zauna ina karanta ma ƙawayena haka in an fita ‘break’ su yi ta yabawa suna faɗin ya yi daɗi ni kuma in ta jin daɗi da ƙara samun kwarin gwiwa. To tun daga lokacin na fara rubuce rubuce har ranar da na san ana rubutawa ta waya, ni ma kawai sai na bi sahu, shi ne har yau ake damawa da ni.
Tun wacce shekara kika fara rubutun ke nan?
Eh to shekarar da na fara rubutu a media zan iya tunawa a shekara ta 2019 ne na fara littafina a media. Amma asalin fara rubutuna na littafi tun a makaranta ne, lokacin ina aji biyu na sakandire a shekara ta 2008.
To wanne littafi ne farko da kika fara rubutawa?
Gaskiya waɗancan da na rubuta a makarantar ba suna, kawai labarin nake rubutawa kara zube. Amma littafinna na farko a media shi ne ‘Gidan Gado’.
Su waɗancan na makarantar daga daya ba ki sabunta su kin musu suna ba?
Gaskiya ban musu ba, saboda littafan da na yi rubutun ma a cikin su duk sun ɓace. Amma lokacin dai ina yin rubutun ne irin labaran yaƙi ɗin nan, domin ni masoyiyar littafan Abdulazeez Sani Madakin gini ce, a da ba wani sabon littafin shi da zai fito ban karanta ba. Saboda kaf cikin marubuta shi ne gwanina.
To yanzu daga fara rubutun ki zuwa yau, kin rubuta littafi guda nawa?
Na rubuta littafai guda bakwai su ne: ‘Gidan Gado’, ‘Wa Zan Aura?’ ‘Sanadin Abayar Sallah’, ‘Boyayiyar Ƙulli’, ‘Gwaji Kafin Aure’, ‘Kisan Ruɗu’, da kuma ‘Baitul Jinn’.
Kin ce littafinki na farko a media shi ne ‘Gidan Gado’, to shi me ya ƙunsa?
To shi littafin ‘Gidan Gado’ na yi shi ne a kan yanayin rayuwa irin ta gidan yawa ɗin nan, gidan gado gidaje irin namu na iyaye da kakanni wato Gidan Gandu. To akwai wata yarinya da ta taso a cikin gidan, tana da farin jini da sauran su haka. Sai wasu daga cikin dangi a gidan suka sa ta a gaba da hassada da dai sauran su, amma daga ƙarshe kuma ita ce ta zama ma dangin nasu fitila. Saboda dama masu iya magana sukan ce hassada ga mai rabo taki ce. Kuma sara da sassaqa ba ya hana gamji tofo.
Kuma cikin waɗannan littafai guda bakwai da kika yi, wanne ne bakandamiyarki a cikin su?
‘Kisan Ruɗu’ saboda shi littafin kisan ruɗu tsantsan cakwakiya ce da cin amana da rikita rikita. Labari ne a kan wata yarinya da kakarta, inda yarinyar ta kai ƙarar kakarta a kan cewa ita ta kashe mata mahaifiya, a gefe guda kuma kakar ta taka sahun ɓarawo, in daya kasance kullum kirarin kakar ke nan a kan cewa ita ce ajalin sirikar tata, da wannan daman aka haɗa baki da ‘yar aka kashe uwar sannan aka maƙala wa kakar cewa ita ta kashe uwar.
Don haka aka dunga tafka shari’a, an ɗauki tsawon lokaci ana shari’a, sai daga ƙarshe kwatsam aka gano uwar bata mutu ba, sai ga ta ta bayyana a gaban kotu. Gaskiya ina son labarin nan domin labari ne da ya ɗauki hankali masu karatu sosai, domin labari ne mai cike da sarƙaƙiya ba za ka tava fahimta labarin ba sai ka kai ƙarshen labarin. Shi ya sa labarin ya samu karɓuwa sosai.
To cikinsu kuma wane ya fi ba ki wahala wajen rubutunsa?
‘Baitul Jinn’ littafin na ɗaya ne da na biyu. Na farkon ‘free’ ne na biyun kuma na kuɗi. Shi yake kan wahalar da ni domin ina saqa zaren labarin ne yana neman kufce mun. Labari ne da ya ƙunshi aljanu da mutane, sannan ya ke nuni ga mutane masu sakaci da ibada, ba su damu da neman ilimi a kan addini ba sai na zamani kawai da rayuwar zamani.
To labarin ne na da tsayi ina shan wahala sosai wajen yin typing, ga shi na karbi kuɗin mutane na kasa ƙarisa musu, ko na ce zan taƙaita shi ba zan iya ba. Ga shi mutane suna matuƙar son labarin, kullum na hau media sai an tambaye ni yaushe zan kammala Baittul jinn part two domin wasu sun ce sai ya yi complete za su siya.
Gaskiya labarin ya ja hankali mutane sosai. Ga labarin ya ƙi bari na sukuni ban kuma iya typing labarin da Asuba kamar yadda nake sauran labaraina sai da daddare kaman irin sha biyun daren nan duk da labari ne mai cike da abubuwan tsoro ni kaina wata ran ina jin tsoro in ina rubuta labarin.
Ke nan da asubah kika fi jin daɗin yin ‘typing’ sai kuma tsakar dare?
Eh gaskiya na fi jin daɗin ‘typing’ da asuba, in kuma ina asibiti ne ina aikin dare to na fi jin daɗin ‘typing’ a lokacin don yana ɗeben kewa ya hana ni jin barci. Gaskiya ni a kowanne yanayi ina iya yin ‘typing’, lokacin da ina cikin bacin rai da damuwa, da kuma cikin farin ciki da walwala duk ina iya yin rubutu.
To kuma ya batun ƙungiyoyin marubuta?
Eh ina cikin Ƙungiyar Arewa writters, sannan ina cikin Ƙungiyar Marubutan Jahar Kaduna.
To daga fara rubutun ki zuwa yau wacce nasara kika cimma ta fuskar rubutu?
Gaskiya nasarorin da na samu ta fannin rubutu ba zai ƙidayu ba, kaɗan daga ciki dai shi ne na haɗu da mutane kala-kala wanda ban taɓa tunani ko mafarkin haɗuwa da su ba, sai ga shi na haɗu da su har mun zauna inuwa ɗaya duk ta sanadin rubutu. Sai wani kyauta da aka taɓa min sanadin rubutuna na ‘Kisan Ruɗu’, ina zaune kwatsam aka kira ni aka ce in zo tasha in karvi wani saƙo na ce saƙon me ke nan aka ce dai in je in karɓa bayan na karɓo saƙon na buɗe na yi matuƙar farin ciki domin saƙo ne da ban taɓa zata ko tunanin samun shi ba a lokacin kuma duk ta sanadin rubutu.
To ya batun ƙalubale?
Eh to ka san a komai bawa yake yi sai ya fuskanci ƙalubale amma ni gaskiya ban wani fuskanci ƙalubale game da fara rubutuna a gida ba ko cikin dangi. Kawai dai sai ɗan ƙalubalen da ba a rasa ba na masu karatu wanda za ka ga wata in ta faɗa ma wani magana tamkar ka bar yin rubutu. Domin na sha fuskantar hakan daga makaranta. Wasu makarantan su ne ciwon kan marubuci.
Wanne kira za ki yi ga ‘yan’uwanki marubuta?
Tom kiran da zan yi ga ‘yan’uwana marubuta shi ne mu ji tsoron Allah mu san cewa marubuta tamkar madubi muke ga al’ummah domin duk abun da muka rubuta a littafanmu yana zamantowa wasu daga cikin al’ummah abun koyi ko abun kallo, saboda haka mu tsaftace alƙalaminmu mu rubuta abubuwa masu muhimmanci wanda ko bayan ranmu zai amfani al’umma bakiɗaya. Daga ƙarshe kuma zan ce Allah ya ƙara haɗa kan marubuta, ya ƙara mana basira da ɗaukaka bakiɗaya.
To wanne saƙo kike da shi ga masoyanki, sannan wacce hanya za ki ba su na haɗuwa da ke don ƙulla zumunci?
Saƙon da zan bayar ga masoyana shi ne ni ma ina matuƙar ƙaunar su a duk in da suke, sannan Sarauniyar kanawa mutun ce mai matuƙar sauƙin kai, da son duk wanda yake ƙaunar ta. Kuma duk wani mai son gani na ko haɗuwa da ni kofa a buɗe take ni mutuniyar Zazzau ce birnin shehu aljannar kanawa, amma mazauniya Kaduna.
To Hajiya Zainab mun gode.
Ni ce da godiya.