Editor

9513 Posts
Matasa na yunƙurin hana zaɓe a Sakkwato

Matasa na yunƙurin hana zaɓe a Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gungun matasa na yunƙurin tada fitina yayin da ake shirin soma zaɓen gwamna da na ’yan majalisar dokoki a Jihar Sakkwato. Ma’aikatan zaɓe sun kwashe kayansu a rumfar zaɓe mai lamba 027 ta Aliyu Kyari kan hatsaniyar da matasa suka tayar suna masu cewar ba su yarda da a yi zaɓen ba. Tun da sanyin safiyar wannan Asabar ɗin dai matasa maza da mata suka fara shiga layi yayin da ma’aikatan zaɓen suka hallara, sai dai kuma gudanar da zaɓen ya gagara a rumfar inda a ƙarshe aka kwashe kayan zaɓe. Daya daga cikin ma’aikatan…
Read More
Gwamna El-Rufai ya shafe awanni a layi domin kaɗa ƙuri’arsa a Kaduna

Gwamna El-Rufai ya shafe awanni a layi domin kaɗa ƙuri’arsa a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shiga jerin gwano domin kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa ta PU024 da ke Unguwan Sarki a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 25 ga watan Febrairu yayin babban zaɓen shugaban ƙasa, El-Rufa'i ya koka da yadda talakawa suka ƙi fitowa kaɗa ƙuri'a a Kaduna, bayan da shafe sama da sa'o'i biyar akan layin kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa, inda ya bayyana damuwarsa kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar. Da yake jawabi…
Read More
Zaɓen Gwamnoni: Na yaba da aikin BVAS – Shugaban NITDA

Zaɓen Gwamnoni: Na yaba da aikin BVAS – Shugaban NITDA

Daga ABUBAKAR M. TAHIR Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi CCIE, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda zaɓen gwamnoni yake cigaba da gudana a faɗin ƙasar nan. Khashifu Inuwa ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da ya kaɗa ƙuriarsa a akwati mai lamba 004 dake 'Yan Dutsina, a mazaɓar Kasuwar Ƙofa dake Hadejia, Jihar Jigawa. Ya ce, "Haƙiƙa na yaba da aikin BVAS mai tantance masu zaɓe, inda cikin ƙasa da daƙiƙa talatin ta yi aikinta jami'an zaɓe suka tantance ni na karɓi katin zaɓena". Ya ƙara da cewa, kowa ya…
Read More
Da Ɗumi-ɗumu: An kama Manajan Darakta na Kano Line bisa zargin tada rikici a rumfar zaɓe

Da Ɗumi-ɗumu: An kama Manajan Darakta na Kano Line bisa zargin tada rikici a rumfar zaɓe

Daga RABIU SANUSI a Kano Jami’an tsaro a Jihar Kano sun damƙe Manajan Darakta na kamfanin sufuri na jihar, Kano Line, wato Bashir Nasiru Aliko Koki, a mazaɓar Masaƙa dake Ƙofar Mazugal a birnin Kano. Ana zarginsa ne da tayar da tarzoma tare da jagorantar ‘yan daba. Ya zuwa haɗa wannan labarin an miƙa Bashir Nasirshi ga 'yan sanda tare da wasu yaransa uku, sannan mutum sama da 200 sun arce.
Read More
Ni ne zan yi nasara a zaɓen Gwamnan Katsina – Raɗɗa

Ni ne zan yi nasara a zaɓen Gwamnan Katsina – Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin jam'iyyar APC, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya ce yana da yaƙinin shi ne zai lashe zaɓen jihar. Raɗɗa ya bayyana haka ne ranar Asabar jim kaɗan bayan da shi da mai ɗakinsa, Hajiya Zulaihat suka kaɗa ƙuri'arsu a mazaɓar Katuka mai lamba 010 da ke mahaifar ɗan takarar dake Ƙaramar Hukumar Charanci ta jihar Katsina. A zantawar da ya yi da manema labarai, Raɗɗa ya ce, "Na zo don kaɗa ƙuri'ata a matsayin haƙƙin ɗan ƙasa. "Ina fata zaɓen zai samar wa al'umar Jihar Katsina shugaba nagari, don…
Read More
Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta samu ƙarin kayan aiki

Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta samu ƙarin kayan aiki

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundundar 'Yan Sandan Jihar Kano ta samu wasu muhimman kayan aiki da za a yi amfani da su wajen Gudanar da zaɓen gwamna a jihar. Daga cikin kayayyakin da Rundundar ta samu sun haɗa jirgin sama mai saukar ungulu wanda zai riƙa shawagi yayin zaɓen. Haka nan, akwai ƙarin jami'an 'yan sanda da kuma motoci da sauransu. Rundundar ta tabbatar wa al'ummar Jihar Kano cewa babu wani mutum da zai samu damar haddasa cikas a yayi zaɓen. Babban Sufeton 'Yan Sanda, Usman Alkali Baba, ya buƙaci rundunar ta yi aiki da kayayyakin yadda ya kamata…
Read More
Ayarin motocin Gwamnan Katsina sun yi hatsari

Ayarin motocin Gwamnan Katsina sun yi hatsari

Daga UMAR GARBA a Katsina Tawagar motocin Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ta yi hatsari a daren jiya juma'a Hatsarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Jiqamshi lokacin da Gwamnan da kuma tawagar motocinsa ke kan hanyar zuwa Ƙaramar Hukumar Ƙafur mahaifar shi inda zai kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen gwamna da na 'yan majalisar jiha ranar Asabar. Rahotannin sun ce jami'an tsaro biyu da ke tare da tawagar, Kabir Adamu da Nura Safiyanu, suka rasa rayukansu a yayin da wasu suka jikkata.
Read More