Editor

9513 Posts
Bayan shafe sa’o’i uku a kan layi, Gwamna El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa

Bayan shafe sa’o’i uku a kan layi, Gwamna El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bayan haƙuri a kan layi na tsawon lokaci, gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sauke nayinsa na jama'a a mazaɓarsa na PU024 da ke Unguwar Sarki GRA a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa. Da yake magana da manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa, El-Rufai ya ce, ana neman masu kaɗa ƙuri’a a yankin Kudancin Kaduna da su zaɓi wata jam’iyya ko kuma su koma gidajensu. Ya ce, a halin yanzu jami’an tsaro na gudanar da bincike a jihar. Gwamnan ya ce, an gudanar da zaɓen a wasu rumfunan zaɓe ba tare da wata matsala ba. “Babu komai,…
Read More
Zaɓen wannan karon ya ɗara wanda ya gabata inganci, in ji Sakkwatawa

Zaɓen wannan karon ya ɗara wanda ya gabata inganci, in ji Sakkwatawa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Yayin da harkokin zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi ke ci gaba da gudana, wasu 'yan ƙasa sun bayyana ra'ayoyinsu game da zaɓen. Ziyarar da wakilinmu ya kai a sassan birnin na Sakkwato, kusan bayanin duka ɗaya ne, inda masu jefa ƙuri'a suka nuna gamsuwarsu. Daga cikin waɗanda wakilin namu ya zanta da su, sun bayyana cewa an samu sauyi a zaɓen wannan karon idan aka kwatanta da zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata. A cewarsu, ingancin zaɓen wannan karon ya ɗara na wanda ya gabata.
Read More
Matawalle ya yaba da haɗin kan da Zamfarawa suka bai wa zaɓen gwamnonin

Matawalle ya yaba da haɗin kan da Zamfarawa suka bai wa zaɓen gwamnonin

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yaba wa masu kaɗa ƙuri'a da suka fito ƙwai da ƙwarƙwata domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen gwamna da na 'yan majalisun jihohi a jihar. Gwamnan ya yi wannan yabon ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’a a mazaɓarsa da ke garin Maradun, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Maradun, a wata hira da manema labarai ranar Asabar. Ya nuna jin daɗinsa da yanayin tsaro a jihar tare da yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, NEC, bisa yadda ta raba kayan zaɓe a kan lokaci a faɗin jihar. "Na yaba da ƙoƙarin…
Read More
INEC ta fara ɗora sakamakon zaɓe a intanet ta BVAS

INEC ta fara ɗora sakamakon zaɓe a intanet ta BVAS

Daga SANI AHMAD GIWA Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ɗora wasu daga cikin sakamakon zaɓen ranar Asabar ta hanyar BVAS. Rashin amfani da BVAS a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu ya haifar da dambarwar amincewa ga hukumar zaɓen, wanda ‘yan Nijeriya da jami’an zave suka yi kakkausar suka. Kodayake hukumar ta yi amfani da matsalar fasaha a matsayin dalilin rashin amfani da BVAS wajen watsa sakamako, da yawa masu suka sun ƙi amincewa da uzurin. Sai dai hukumar ta yi alƙawarin inganta tare da yin amfani da na'urar a zaɓen da ke gudana yau. Manhaja ta…
Read More
Yadda jadawalin gasar Europa ya kasance

Yadda jadawalin gasar Europa ya kasance

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An kammala zagayen ’yan 16 na gasar Europa, inda a yanzu ƙungiyoyi 8 suka samu damar tsallakawa zagayen daf da na kusa da na ƙarshe a gasar. Manchester United da Sevilla za su kara a wasan quarter final a gasar zakarun Turai ta Europa League. Ƙungiyoyin da suka kai wannan mataki sun haɗa da Sporting Lisbon da Feyenoord da Juventus da Manchester United da Roma da Sevilla da Union Saint-Gilloise sai kuma Bayer Leverkusen. Arsenal da aka saran za ta taɓuka abin azo a gani a gasar ta bana, ganin irin tagomashin da ta ke samu…
Read More
An kama mabaraci da tsabar kuɗi Naira miliyan 37.3 ɓoye cikin ƙafafun roba

An kama mabaraci da tsabar kuɗi Naira miliyan 37.3 ɓoye cikin ƙafafun roba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jami’an ’Yan Sandan Dubai sun kama wani mabaraci da ya bayyana a matsayin wanda aka yanke wa ƙafa, ɓoye da tsabar kuɗi $81k kwatankwacin Naira miliyan 37.3 a cikin jabun ƙafafun roban. A cewar jaridar Gulf News, mutumin da ya shiga ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da takardar bizar ziyara an kama shi ne a ranar Alhamis 16 ga Maris, 2023, inda yake roƙon sadaka a kusa da masallatai da kuma wuraren zama. An tattaro cewa mabaracin bayan kama shi an miƙa shi zuwa gaban kotu na Dubai. ’Yan sandan Dubai sun gargaɗi jama’a da kada su…
Read More