Editor

9513 Posts
Jam’iyyar PDP ta lallasa APC a gidan gwamnatin Kaduna

Jam’iyyar PDP ta lallasa APC a gidan gwamnatin Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kaduna ta sha kaye a akwatunan zaɓe biyun da ke Gidan Sir Kashim Ibrahim, fadar gwamnatin jihar. Ɗan takarar gwamna na PDP, Alhaji Isa Ashiru Kudan ne ya lashe akwati mai lamba 014 da ƙuri’u 77 yayin da ɗan takarar APC, Sanata Uba Sani ya samu ƙuri’u 40. Jami’in zaɓe Mohammed Baso ya ce jam’iyyun PRP da NNPP sun samu ƙuri’u ɗai-ɗaya. Haka ma akwatu mai lamba 013 PDP ta yi nasara da ƙuri’u 69 yayinda APC ta samu 64. Jami’in zaɓe Kalu Kelechi Michael ya ce jam’iyyar LP ta samu…
Read More
Ya kamata Gwamnati ta ƙarfafa tsaron ƙasa da karin jami’ai – Tambuwal

Ya kamata Gwamnati ta ƙarfafa tsaron ƙasa da karin jami’ai – Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da ƙarin jami’an tsaro domin tallafawa wajen ƙarfafa lamarin tsaro a faɗin ƙasar nan. Tambuwal ya bayar da shawarar haka ne jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa a rumfa mai lamba 33 dake Makarantar Sakandirin garin Tambuwal. A cewarsa, samar da ƙarin jami’an tsaron ba makawa zai taimaka wajen kare martabar ƙasar a idon duniya. Game da zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi kuwa, Tambuwal ya buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, da ta ƙara yin shiri na musamman domin gudanar da…
Read More
INEC ta ɗage zaɓen gwamna zuwa Lahadi a rumfunan zaɓe 10 a Legas

INEC ta ɗage zaɓen gwamna zuwa Lahadi a rumfunan zaɓe 10 a Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ɗage zaɓen gwamna da na majalisar jiha a wasu rumfunan zaɓe guda 10 a yankin Lekki, Jihar Legas. Kwamishinan INEC na jihar, Segun Agbaje, shi ne ya sanar da haka ga manema labarai. A cewarsa, wasu masu yi wa ƙasa hidima da INEC ta ɗauka aikin wucin-gadi sun yi zargin an kama su yayin zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata yayin da suka yi yinƙurin shiga yankin. Ya ce bayan da ma'aikatansu suka shirya kayan aiki, mazauna yankin sun ji tsoron fitowa gudun kada ɓata-garin yankin su fafare su, su tarwatsa…
Read More
Tsohon Mataimakin Gwamnan Ekiti ya mutu a ranar zaɓe

Tsohon Mataimakin Gwamnan Ekiti ya mutu a ranar zaɓe

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti na baya-bayan nan, Otunba Bisi Egbeyemi, rasuwa a ranar Asabar da ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi. Egbeyemi ya rasu ne da safiyar Asabar a wani asibiti da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar. An haifi marigayin ne ran 8 ga Mayu, 1944, inda ya bar duniya yana da shekara 79. A halin rayuwarsa, lauya ne shi kuma ɗan siyasa. Ya taɓa riƙe matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Ado Ekiti daga 1992 zuwa 1993, kafin daga bisani ya zama Mataimakin Gwamnan jihar ga Gwamna Kayode Fayemi, daga 2018…
Read More
Wata mata ta ci na-jaki a wajen zaɓe a Kano

Wata mata ta ci na-jaki a wajen zaɓe a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Masu kaɗa ƙuri'a sun lakaɗa wa wata mata duka a wajen zaɓe bisa zarginta da aka yi da sayen ƙuri'a. Lamarin ya faru ne a Ado Yola Primary School fa ke mazaɓar Na'ibawa cikin Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano. Da aka nemi jin ta bakinta, matar ta ce kuɗin mota ta bayar ba kuɗin sayen ƙuri'a ba kamar yadda aka yi zargi.
Read More
Ɗan takarar gwamnan NNPP a Katsina ya tsallake rijiya da baya

Ɗan takarar gwamnan NNPP a Katsina ya tsallake rijiya da baya

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP, Eng. Nura Khalil, ya tsallake rijiya da baya a hanyarsa ta zuwa Ƙaramar Hukumar Bakori inda zai kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen gwamna da na 'yan majalisar jihohi da ke gudana. Ɗan takarar ya ce 'yan ta'adda ɗauke da makamai sun tare hanyar da tawagarsa za ta bi don zuwa mazaɓar tasa. "Mun wuce Ƙanƙara daidai mararrabar Katikawa sai muka ga ana tsaida mu, muka tsaya sai ga wani mutum ya zo 'yan ta'adda sun fasa masa kai," Inji shi. Ya ce wasu sun gaya masu cewar akwai…
Read More
‘Yan daba sun farmaki ma’aikacin gidan rediyo a Kano

‘Yan daba sun farmaki ma’aikacin gidan rediyo a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Wasu 'yan dabar siyasa sun farmaki wani ma'aikacin gidan Rediyon Premier mai suna Ashiru Umar a lokacin da yake tsaka da aiki a mazaɓar Galadima Primary School cikin ƙaramar hukumar Gwale a Kano. Rahotanni da dama sun yi nuni da matsalar ta fara ne a lokacin da 'yan dabar siyasar suka kai masa hari inda suka yi tunanin yana ɗaukar su hoto yayin da suke raba wa masu kaɗa ƙuri'a kuɗi a rumfar zaɓe. Ashiru Umar Wanda aka yi wa rauni tare da yaga masa kaya, ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da ya…
Read More
Ubangiji Ya riga ya zaɓi wanda zai zama Gwamnan Kano – Gawuna

Ubangiji Ya riga ya zaɓi wanda zai zama Gwamnan Kano – Gawuna

Daga RABI'U SANUSI a Kano. Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa Allah Ya riga ya zaɓi wanda zai zama gwamna a Jihar Kano tun fil azal. Gawuna ya bayyana haka ne yayin da yake kaɗa ƙuri'arsa da safiyar Asabar a mazaɓarsa dake Gidan Nasiru Ahli dake Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano. Ya ce yana da tabbacin samun nasara a wannan zaɓe wanda a cewarsa yana gudana cikin kwanciyar hankali. "Ba zan yi ƙasa a gwuiwa ba wajen cewa Ubangiji ke ba da mulki, mun kuma yi zaɓe kamar yadda mutane suka…
Read More
’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wuraren zaɓe a Legas

’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wuraren zaɓe a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mutum ɗaya ya rasa ransa, wasu da dama sun samu raunuka bayan da ’yan daba suka kai farmaki a rumufunan zaɓe a sassan Jihar Legas. An gano cewa an bindige mutum ɗaya har lahira, wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da ɓata-garin suka yi dirar mikiya a wuraren zaɓen. Yankunan da aka kai hare-haren sun haɗa da Ikota, Jakande, Ijegun, Festac da kuma Isolo. Rikicin ya fara ɓarkewa ne bayan ɓata-garin sun kutsa cikin yankin Okota, inda jam’iyyar LP ke da ƙarfi. Maharan sun fatattaki mutanen da suka fito yin kaɗa ƙuri'a, sannan suka…
Read More