Editor

9513 Posts
‘Yan sanda a Kano sun gabatar da mutum 161 da suka kama da aikata laifukan zaɓe

‘Yan sanda a Kano sun gabatar da mutum 161 da suka kama da aikata laifukan zaɓe

Daga BASHIR ISAH Hukumar 'yan sanda a Jihar Kano ta cafke mutum 161 kan laifin ƙwacen akwatin zaɓe da sauran laifuka da suka danganci zaɓen. Kwamishinan 'Yan Sandan Kano, Muhammad Gumel, shi ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da waɗanda aka kaman ga manema labarai ranar Lahadi a Kano. Ya ce sun kama waɗanda lamarin ya shafa ne yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi ranar Asabar a jihar. Ya ce baya ga satar akwatin zaɓe, an kama wasunsu bisa zargin sayen ƙuri'a da kuma yunƙurin cinna wa ofishin INEC wuta a jihar. Ya…
Read More
‘Yan jarida sun yi barazanar ƙaurace wa tattara sakamakon zaɓe a Kano

‘Yan jarida sun yi barazanar ƙaurace wa tattara sakamakon zaɓe a Kano

Daga WAKILINMU 'Yan jarida a Jihar Kano sun zargi Hukumar Zaɓe, INEC, da zaɓen 'yan tsiraru daga abokan aikinsu don sa ido kan sha'anin tattara sakamakon zaɓen gwamna da na majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar Asabar. Da wannan 'yan jaridar suka yi barazanar ƙaurace wa aikin tattara sakamakon zaɓen muddin ba a ɗauki matakin gyara nan take ba. Sanarwar da Jami'in Hulɗa da Jama'a na INEC, Adam Maulud, ya fitar ta nuna wasu 'yan tsirarun 'yan jarida aka yarda su lura yadda aikin tattara sakamakon zai gudana a ranar Lahadi. INEC ta shirya soma tattara sakamakon zaɓen…
Read More
Zaɓen Gwamnoni: Gwamna Makinde ya kai bantensa

Zaɓen Gwamnoni: Gwamna Makinde ya kai bantensa

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ƙarƙashin Jam'iyyar PDP. Makinde ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 563,617 yayin da Sanata Teslim Folarin na APC ya rufa masa baya da ƙuri'u 251,230, sannan Adebayo Adelabu na jam'iyyar of the Accord ya zo na uku inda ya tsira da ƙuri'u 38,757. A ranar Asabar aka gudanar da zaɓen gwamna a jihohi 28 daga cikin 36 da ƙasar ke da su. Jihohi takwas ɗin da ba a yi zaɓen gwamna a cikinsu ba sun haɗa…
Read More
Ƙananan hukumomi 8 sun gabatar da sakamakon zaɓen gwamna a Sakkwato

Ƙananan hukumomi 8 sun gabatar da sakamakon zaɓen gwamna a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ya zuwa yanzu ƙananan hukumomi takwas daga cikin 23 ne suka gabatar da sakamakon zaɓukkansu. Ƙananan hukumomin sun haɗa da Binji wanda APC ta samu ƙuri'u dubu 13,410 yayin da PDP ke biye mata da ƙuri'u 11,078, sai kuma ƙaramar hukumar Wurno inda APC ke da ƙuri'u 17,350 sannan PDP na da 13,099. Sai kuma ƙaramar hukumar Yabo da jamiyyar APC ta samu ƙuri'u 14,729 inda PDP ta tashi da ƙuri'u 12,014. Haka lamarin yake a ƙaramar hukumar Isa, inda ɗan takarar APC, Ahmad Aliyu, ya doke abokin karawarsa Malam Saidu Umar da ƙuri'u 13,632,…
Read More
PDP ta ƙwace kujerar Kakakin Majalisar dDokokin Yobe da ta mahaifar shugaban Majisar Dattawa

PDP ta ƙwace kujerar Kakakin Majalisar dDokokin Yobe da ta mahaifar shugaban Majisar Dattawa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Sakamakon da hukumar zaɓe INEC ta sanar na zaɓen 'yan majalisar dokokin jihar Yobe, ya nuna ɗan takarar jam'iyyar PDP, Hon. Musa Lawan Majakura ya lallasa na jam'iyyar APC, wanda shi ne Kakakin majalisar, Hon. Ahmed Lawan Mirwa a mazaɓar Nguru ta waje. Sakamakon ya nuna jam'iyyar PDP ta samu ƙuri'u 6,648 yayin da APC ta samu ƙuri'u 6,466 a zaɓen, wanda hakan ya bai wa ɗan takarar PDP nasarar lashe zaɓen. Hon. Majakura na PDP ya lallasa Hon. Ahmed Mirwa ne bayan da ya kwashe shekaru 20 yana jan zarensa a kujerar, daga 2003…
Read More
Rundunar ‘Yan Sanda ta haramta bikin murnar lashe zaɓe a Kano

Rundunar ‘Yan Sanda ta haramta bikin murnar lashe zaɓe a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Usaini Mohammed Gumel mai jagorantar harkokin zaɓen da ke gudana a jihar, ta haramta bikin murnar lashe ta hanyar zagaye kan tituna ko makamancin haka wanda ka iya haifar da hargitsi a jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ga manema labarai a yammacin Asabar bayan kammala zagayen da haɗakar rundunonin tsaro suka gabatar na sa ido bisa yadda dokar Hukumar 'Yan Sanda ta Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin IG Usman Baba Alkali ta ɗora ma kowane CP a faɗin ƙasar a lokacin zaɓen. CP Gumel ya kuma yaba da yadda…
Read More
ICPC ta kama masu sayen ƙuri’a a Katsina da Sakkwato

ICPC ta kama masu sayen ƙuri’a a Katsina da Sakkwato

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar yaƙi da cin hanci da almundahanar kuɗaɗe ta Nijeriya, wato ICPC, ta ce jami'anta sun kama mutum huɗu bisa zargin sayen ƙuri'a a jihohin Sakkwato da Katsina. ICPC ta bayyana haka ne cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Tiwita, inda ta ce ta kama mutanen ne ranar Asabar a lokacin da ake gudanar da zaɓen gwamna da na 'yan majalisar dokokin jihohi. Haka kuma, hukumar ta ce an kai wa jami'anta hari tare da raunata mutum guda a jihar Sakkwato. Ta ƙara da cewa an kai wa jami'an nata harin ne…
Read More
Gobara ta ƙara lamushe shahararriyar kasuwa a Borno

Gobara ta ƙara lamushe shahararriyar kasuwa a Borno

Daga AMINA YUSUF ALI Gobara ta lamushe wata kasuwa da ake kira Gamboru a cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Kasuwar Gamboru ita ce kasuwar sayar da kayan gwari mafi girma a garin Maiduguri. Ya zuwa haɗa wannan labari ba a san musabbabin gobarar ba, amma majiyarmu ta bayyana cewa, an rasa dukiya ta ɗaruruwan miliyoyin Nairori. Gobarar ta afku ne bayan ɓarkewar wata gobarar daban a sassafiyar Asabar ɗin a kasuwar Biu da ke a Kudancin jihar Borno.
Read More
Zaɓen Gwamnoni: APC ta lallasa PDP a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa

Zaɓen Gwamnoni: APC ta lallasa PDP a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu A ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen Gwamna da na 'yan majalisun dokoki, wanda malamar zaɓe a rumfa mai lamba 001 dake cikin Makaranar Firamaren Katuzu, a Gashuwa ta jihar Yobe ta jagoranta, Shugaban Majisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya lashe mazaɓarsa da tazara mai yawa a zaɓen. Da take bayyana sakamakon, jami'ar zaɓen, Malama Rahama Ahmad ta ce ɗan takarar Gwamna a jam'iyyar APC shi ne ya samu gagarumar nasara a rumfar zaɓen da yawan ƙuri'a 435 yayin da abokin takararsa na PDP ya samu ƙuri'a 295.
Read More
Masu sayen ƙuri’a sun kai wa jami’an EFCC hari a Kaduna

Masu sayen ƙuri’a sun kai wa jami’an EFCC hari a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An kai wa jami’an EFCC hari a yayin da suka ƙara matsa lamba kan aikin sanya idanu a zaɓen da ake gudanarwa na gwamnoni da ’yan majalisun jihohi. Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce, an kai wa jami’an nata hari ne a Unguwar Rimi yayin da suke yunƙurin kama wasu da ake zargi da sayen ƙuri’a. Tawagar tasu da ke aikin sanya idanu na sirri ta yi zargin wani mutum da ake kira Kabiru Musa da aka gani cikin wani bidiyo riƙe da wayarsa yana aikawa mutane kuɗi idan…
Read More