ICPC ta kama masu sayen ƙuri’a a Katsina da Sakkwato

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumar yaƙi da cin hanci da almundahanar kuɗaɗe ta Nijeriya, wato ICPC, ta ce jami’anta sun kama mutum huɗu bisa zargin sayen ƙuri’a a jihohin Sakkwato da Katsina.

ICPC ta bayyana haka ne cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Tiwita, inda ta ce ta kama mutanen ne ranar Asabar a lokacin da ake gudanar da zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.

Haka kuma, hukumar ta ce an kai wa jami’anta hari tare da raunata mutum guda a jihar Sakkwato.

Ta ƙara da cewa an kai wa jami’an nata harin ne a daidai lokacin da ta kama mutum uku masu sayen ƙuri’a yayin zaɓen.