Editor

9513 Posts
Duk dillalin da ya ƙara farashin kayayyaki a bakin lasisinsa – BUA

Duk dillalin da ya ƙara farashin kayayyaki a bakin lasisinsa – BUA

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya yi barazanar ƙwace lasisin duk wani dillalin kamfanin da aka kama ya tsawwala farashin kayayyaki yayin watan Ramadan. Alhaji Abdulsamad Rabiu ya bai wa al'umma tabbacin kamfaninsa ya tanadi wadatattun kayayyakin masarufin da za su ishi ɗaukacin jihohin ƙasar nan a lokacin Ramadan da kuma bayansa da zummar hana faruwar matsin da 'yan ƙasa kan fuskanta da zarar watan Ramadan ya kama. Shugaban BUA ya bayyana haka ne ta bakin wakilinsa na yankin Arewa, Alhaji Mohammad Adakawa, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kano.…
Read More
Jonathan ya ƙaddamar da hanya a Bauchi

Jonathan ya ƙaddamar da hanya a Bauchi

Daga AISHA ASAS A Talatar da ta gabata Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ƙaddamar da babbar hanya ta farko wadda Gwamna Bala Mohammed ya gina a Bauchi. Hanyar wadda ta haɗa garin Sabon Ƙaura da ƙauyen Miri, na daga cikin hanyoyin farko-farko da gwamnan ya bada aikinsu a kwanaki 100 na farko da ya yi a kan mulki. Sa'ilin da yake jawabi yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Bala ya ce sabuwar hanyar da aka gina mai nisan kilomita 6.2, an bada kwangilar ne kan kuɗi Naira bilyan N2. Daga nan, ya yaba wa Jonathan bisa ɗora shi kan hanya mai…
Read More
Ƙa’idojin Azumin Ramadan

Ƙa’idojin Azumin Ramadan

Daga RIDWAN SULAIMAN Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinƙai ‘Yan’uwa maza da mata a Musulunci, huɗubarmu ta yau za ta yi magana ne a kan ƙa’idojin da ke tattare da azumin Ramadan. ‘Yan’uwa maza da mata a Musulunci, yanzu abin da ya rage tsakaninmu da Ramadan wasu ‘yan kwanaki ne, don haka ya kamata mu tunatar da kawunanmu dangane da ƙa’idojin da Ramadan ke tattare da su domin samun tarin sakamako a watan da ke zuwa sau guda a shekara - wa ya sani ko wannan ya zama shi ne Ramadan na ƙarshe a wannan rayuwa! An farlanta yin…
Read More
Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Daga WAKILINMU Koriya ta Arewa ta bada sanarwar ba za ta halarci gasar Olympics da aka shirya gudanarwa a Ƙasar Tokyo ba a cikin wannan shekara saboda dalili na neman kare 'yan wasanta daga kamuwa da cutar korona. Koriya ta Arewa ta ce na musamman ta ɗauki wannan mataki domin kare 'yan wasanta gudun kada su harbu da cutar korona. Wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya katse wa Koriya ta Kudu damar da ta hango na yin amfani da gasar wajen tattaunawa da takwararta Koriya ta Arewa game da abin da ya shafi kan iyaka. A 2018 ƙasashen biyu…
Read More
Al’ummar Arewa-maso-gabas sun roƙi Buhari da ya inganta tsaron yankinsu

Al’ummar Arewa-maso-gabas sun roƙi Buhari da ya inganta tsaron yankinsu

Daga UAMR M. GOMBE 'Yan gudun hijira a yankin Arewa-maso-gabas sun roƙi gwamnati da ta taimaka ta maido da zaman lafiya a yankinsu domin ba su damar komawa gidajensu don ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba a can baya. 'Yan gudun hijirar sun koka kan yadda rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita su tare da jefa su cikin mawuyacin halin rayuwa, lamarin da ya sa suke shakku kan ko gwamnatin za ta iya maida su matugunansu na asali. Wata sanarwa da 'yan gudun hijirar suka fitar a ƙarkashin Taron 'Yan Gudun Hijira na Yankin Arewa-maso-gabas wadda Manhaja ta mallaki…
Read More
Imo: Yadda IPOB ta kai hari kan gidan yari da hedikwatar ‘yan sanda

Imo: Yadda IPOB ta kai hari kan gidan yari da hedikwatar ‘yan sanda

Daga WAKILINMU 'Yan Ƙungiyar Jama'ar Biafra (IPOB) sun kai mummunan hari kan ofishin 'yan sanda da kuma gidan yari a Owerri babban birnin jihar Imo, inda suka yi sanadiyar tserewar fursunoni da dama 'Yan ƙungiyar wanda da ma ana zarginsu da kashe jami'an tsaro a shiyyar Kudu-maso-gabas, sun kai harin ne ta hanyar banka wuta a gine-gine da motoci da sauran kayayyaki. Majiyar Manhaja ta ce maharan sun yi amfani da abubuwa masu fashewa da kuma bindigogi wajen kai harin. Ta ci gaba da cewa an ji fashewa mai ƙara da kuma harbe-harben bindiga a yankin. Yayin harin, wasu daga…
Read More

Kaduna: ‘Ba mu wakilta kowa don sasantawa da ‘yan fashi ba’ – Aruwan

El-Rufai Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin hukunta duk wanda ta kama yana sasantawa da 'yan fashi ko 'yan ta'adda a jihar. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata. Kwamishinan ya ce Gwamnatin Kaduna ba ta wakilta kowa ba don shiga tsakaninta da 'yan fashi, tare da ƙaryata rahoton da ke cewa Gwamnatin Nasir El-Rufai ta naɗa wasu wakilai domin tattaunawa da masu aikata muggan laifuka a jihar. Sanarwar Kwamishinan ta buƙaci 'yan jihar da su kai rahoton…
Read More
Gumi da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Gumi da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Daga FATUHU MUSTAPHA Fitaccen malamin Islman nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi wata ganawar sirri tare da Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta babban birnin jihar Ogun, a Lahadin da ta gabata. Wata majiya ta kusa da taron, ta ce Gumi ya zaɓi ganawa da Chief Obasanjo ne kasancewarsa na mai faɗa a ji a cikin ƙasa kuma wanda al'umma ke girmamawa. Malamin ya labarta wa Obasanjo ziyarar da ya kai wa Fulani masu fashi a Arewacin ƙasa da zummar gwamnati ta yi wa yanayin kyakkyawar fahimta da kuma yin aiki da shawarwarin da…
Read More