Editor

9513 Posts

Gwamnan Zamfara ya bayyana takaici kan gallaza wa ’yan Arewa

Gwamna Matawalle Daga FATUHU MUSTAPHA a Abuja A Alhamis da ta gabata Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Bello, Matawallen Muradun, ya fitar da wata doguwar ƙasida da yake nuna takaicinsa a game da yadda abubuwa suke tafiya a Nijeriya musamman kan yadda ake gallaza wa ’yan Arewa wasu yankunan ƙasar. Ƙasidar da aka raba ta ga manema labarai, tana ɗauke da sa hannun gwamnan na jihar Zamfara kai tsaye ne, inda ya nuna yana cike da alhini a game da yadda abubuwa suke ƙara tavarɓarewa a ƙasar. "Na rubuta wannan ƙasida ne a matsayina na jagora kuma ɗan Arewa, domin wannan ba lokaci…
Read More
Yayin da watan Azumi ya ƙarato

Yayin da watan Azumi ya ƙarato

A makon da za mu ne ake sa ran ɗaukar azumin watan Ramadan, wata mai alfarma ga dukkan Musulmin duniya. A ranakun wannan wata, waxanda suke kamawa guda 29 ko 30 a kowacce shekara, Musulmi sukan kaxaita daga aikata wasu muhimman abubuwa a rayuwar ɗan adam da rana, kamar ci, sha da jima’i. Lokacin haramcin hakan yana kamawa ne daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana a kulliyaumin. To, a zahirin gaskiya ba waɗannan abubuwa ne kaɗai abubuwan da ake sa ran Musulmi ya guje su ba, illa dai kawai za a iya cewa, waɗannan abubuwa guda uku, wato ci, sha…
Read More
Kwara: An samu ɓarkewar rikicin kabilanci a ƙaramar hukumar Edu

Kwara: An samu ɓarkewar rikicin kabilanci a ƙaramar hukumar Edu

Daga AISHA ASAS Bayanan da Manhaja ta samu daga jihar Kwara sun nuna an samu ɓarkewar rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummar Tsaragi da maƙwabtansu na Kange a yankin ƙaramar hukumar Edu, lamarin da ya yi sanadiyar mutane da dama sun ji rauni. Duk da dai ba aka ga fayyace dalilin aukuwar rikicin ba ya zuwa haɗa wannan labari, amma binciken Manhaja ya gano babu ko mutum guda da ya rasa ransa sakamakon rikicin wanda ya faru a ranar Alhamis. Sai dai wata shaida ta tabbatar cewa an samu mutane da dama daga ɓangarorin biyu waɗanda suka jikkata yayin hatsaniyar. Jami'i mai…
Read More
Kaduna: NLC ta nuna rashin amincewarta kan matakin sallamar ma’aikata

Kaduna: NLC ta nuna rashin amincewarta kan matakin sallamar ma’aikata

Daga FATUHU MUSTAPHA Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta ƙi amincewa da shirin korar ma'aikata da maida wasunsu ma'aikatan wucin-gadi a jihar. Ƙungiyar na ra'ayin cewa ɗaukar wanna mataki zai ƙara tsananta matsalar tsaro da kuma ƙalubalen tattalin arzikin da ake fama da su a jihar. Da suke yi wa manema labarai bayani kan batun jim kaɗan bayan kammala taron shugabannin ƙungiyar na jiha, Shugaban NLC na Kaduna, Comrade Ayuba Magaji Suleiman da Sakatariyarsa Comrade Christiana John Bawa, baki ɗaya sun yi kira ga gwamnatin Kaduna da ta janye wannan shiri nata sannan ta lalubo hanyar da…
Read More

Imo: ‘Yan bindiga sun sake kai hari a ofishin ‘yan sanda

Harin da aka kai wa gidan yarin Owerri Daga WAKILINMU 'Yan bindiga a jihar Imo sun kai hari a babban ofishin 'yan sanda na Mbieri cikin yankin ƙaramar hukumar a jihar Imo. Harin wanda ya auku ranar Laraba da tsakar dare, ha yi sanadiyar tserewar wasu da ake tsare da su a ofishin. Jami'in Hulɗa da Jama'a na 'Yan Sandan Jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda ya ce ɗaya daga cikin jami'ansu ya ɓata yayin da wasu jamiai biyu sun ji rauni sakamakon farmakin. Haka nan, Ikeokwu ya tabbatar cewa maharan sun kuɓutar da wasu da ake…
Read More

Haramtattun makamai sama da milyan 6 ake ta’ammali da su a Nijeriya – Abdulsalam

Andulsalam Daga UMAR M. GOMBE Tsohon Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Zaman Lafiyar Ƙasa, General Abdulsalami Abubakar (mai murabus) ya yi jan hankali a kan yadda ta'ammali da bindigogi ke daɗa ƙaruwa a Nijeriya. Yana mai cewa a halin da ake ciki a ƙiyasce bindigogi milyan shida ne ake ta'ammali da su a faɗin ƙasa ba a bisa ƙa'ida ba. Abdulsalam ya ce ƙaruwar ta'ammali da makamai ya tsananta matsalar tsaro a ƙasa wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 80,000 tare da raba mutane kusan milyan uku da gidajensu. Abubakar ya yi waɗannan bayanai ne a wajen…
Read More

Buhari ya buƙaci sabon Sarkin Kagara ya zamo mai yi wa talakawansa hidima

Garba Gunna Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Alhaji Ahmad Garba Gunna murna bisa naɗa shi da aka yi a matsayin sabon Sarkin Kagara da Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello ya yi. Kafin naɗin nasa, Garba Gunna shi ne shugaban hukumar tara haraji na jihar Neja. Buhari ya yi kira ga sabon sarkin da ya yi amfani da sanin da yake da shi wajen yi wa talakawan masarautarsa hidima da kuma kawo wa masarautar cigaba. Kazalika, Buhari ya buƙaci basaraken da ya yi amfani da matsayinsa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'arsa, tare da jaddada cewa masarautu na da…
Read More
Jami’an tsaro sun tarwatsa maɓuyar ɓatagari a Akwa Ibom

Jami’an tsaro sun tarwatsa maɓuyar ɓatagari a Akwa Ibom

Daga WAKILINMU Rundunar haɗin gwiwa ta jami'an tsaro a jihar Akwa Ibom, ta yi nasarar tarwatsa maɓuyar wasu ɓatagari a yankin Ntak Ikot Akpan a jihar. Sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Hulɗa da Jama'a na Sojoji, Brig. Gen. Mohammed Yerima, ta nuna ƙura ta lafa a yankin, yayin da kuma 'yansanda na ci gaba da sa-ido don bai wa jama'ar yankin damar ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wani tsoro ko fargaba ba. Yerima ya buƙaci jama'a da su kwantar da hankulansu kana su ci gaba da bai wa jami'an tsaro haɗin kai don samun…
Read More
Wasanni: Dare ya gargaɗi ‘yan wasa su guji yin amfani da muggan ƙwayoyi

Wasanni: Dare ya gargaɗi ‘yan wasa su guji yin amfani da muggan ƙwayoyi

Daga BASHIR ISAH Ministan Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare, ya yi kira ga 'yan wasa da su guji yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari da duk wani nau'i na fitina. Ministan ya yi wannan kira ne yayin rangadin da ya je don duba wuraren wasanni na bikin wasannin motsa jiki na ƙasa (NSF) karo na 20 da ke gudana a Benin, babban birnin jihar Edo. Dare wanda shi ne ya wakilci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo a wajen taron buɗe bikin, ya ce bikin zai taimaka wajen gano 'yan ƙasa masu fasaha a sha'anin wasannin motsa jiki. Binciken Manhaja…
Read More
An naɗa Baba a matsayin muƙaddashin IGP

An naɗa Baba a matsayin muƙaddashin IGP

Daga UMAR M. GOMBE A halin da ake ciki, Alkali Baba ya zama muƙaddashin Babban Sufeton 'Yan Sandan Nijeriya. (IGP). Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci bikin naɗa sabon muƙaddashin a ranar Laraba kuma a Fadar Shugaban Ƙasa da ke birnin tarayya, Abuja. Wa'adin Mohammed Adamu a matsayin shugaban rundunar ya ƙare ne a Fabrairun da ya gabata bayan da ya cika shekara 35 da aiki. Inda daga bisani Shugaba Buhari ya ƙara masa watanni uku. Waɗanda suka halarci bikin naɗin har da tsohon IGP Mohammed Adamu; Sakataren Gwamnantin Tarayya (SGF); Boss Mustapha; Ministan Harkokin 'Yansanda, Maigari…
Read More