10
Apr
Buhari Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa ta'aziyyarsa ga Sarauniya Elizabeth II ta Ingila dangane da rasuwar mijinta Yarima Philip wanda ya bar duniya yana da shekara 99. Buhari ya ce, "rasuwar marigayin alama ce ta ƙarshen wani ƙarni. Yarima Philip ya kasance mutum mai muhimmanci wanda duniya ma ta san da shi, wanda ba za a mance da gudunmawarsa ga ƙasashe renon Ingila ba na tsawon zamunna. "Yarima Philip ya kasance jarumi ne wanda ya yi amfani da dukiyarsa wajen tallafa wa al'umma musamman ma abin da ya shafi tsare gandun daji da sha'anin matasa…
