Editor

9513 Posts

‘Operation Lafiya Dole’ ta nemi haɗin kan ‘yan jarida

Daga FATUHU MUSTAPHA Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Major-General Faruk Yahaya, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su mara wa jami'an tsaro baya domin kawo ƙarshen Boko Haram a Nijeriya. Kwamandan ya yi wannan kira ne yayin wani taron karramawa da aka shirya wa 'yan jarida a Barno a barikin sojoji da ke Maimalari a jihar. General Yahaya ya nuna yabo tare da jinjina ga 'yan jarida inda ya bayyana su a matsayin masu taka muhimmiyar rawa a fagen yaƙi da ta'addanci da ake ci gaba da fafatawa. Ya ci gaba da cewa kafafen yaɗa labarai na da…
Read More

Ramadan: NSCIA ta buƙaci Musulmi su saurari ta bakin Sarkin Musulmi

Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta buƙaci al'ummar Nijeriya da su kasance cikin shiri don jin ta bakin Sarkin Musulmi kuma shugaban NSCIA na ƙasa dangane da soma azumin Ramadan na 1442 AH. Cikin sanarwar da ta fitar a Lahadin da ta gabata ta hannun Daraktan Gudanarwa, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, NSCIA ta buƙaci al'ummar Musulmi su zamo masu himma wajen gabatar da addu'o'i ga Allah musamman ma a watan Ramadan don alherin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya. NSCIA ta ƙarfafa buƙatar neman watan…
Read More
Jonathan ya ƙaddamar da hanya a Bauchi

Jonathan ya ƙaddamar da hanya a Bauchi

Daga AISHA ASAS A Talatar da ta gabata Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ƙaddamar da babbar hanya ta farko wadda Gwamna Bala Mohammed ya gina a Bauchi. Hanyar wadda ta haɗa garin Sabon Ƙaura da ƙauyen Miri, na daga cikin hanyoyin farko-farko da gwamnan ya bada aikinsu a kwanaki 100 na farko da ya yi a kan mulki. Sa'ilin da yake jawabi yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Bala ya ce sabuwar hanyar da aka gina mai nisan kilomita 6.2, an bada kwangilar ne kan kuɗi Naira bilyan N2. Daga nan, ya yaba wa Jonathan bisa ɗora shi kan hanya mai…
Read More

Da ɗumi-ɗuminsa: Likitoci sun janye yajin aiki

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NARD) Uyilawa Okhuaihesuyu, ya bada sanarwar janye yajin aikin sai baba ta gani da suka shiga. Likitocin sun tsunduma yajin aikin ne tun a ranar 1 ga Afrilun da ya gabata. Matakin shiga yajin aikin da likitocin suka ɗauka ya jefa asibitocin ƙasar nan cikin mawuyacin hali, lamarin da ya  haifar wa marasa lafiya cikas na rashin samun kulawar da ta dace a asibitocin. Kodayake dai likitocin sun janye yajin aikin ne bisa sharaɗin cewa idan Gwamnantin Tarayya ta gagara biya musu buƙatunsu, to fa za su koma su ci gaba daga inda…
Read More

Zimbabwe: Ɗalibai 106 sun kamu da cutar korona cikin sa’o’i 24

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Zimbabwe sun nuna ya zuwa ranar Alhamis da ta gabata, an samu ɗalibai 106 daga wasu makarantun ƙasar guda biyu da suka harbu da cutar korona a cikin yini guda. Sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa ɗalibai 51 sun kamu da cutar daga makarantar Sacred Heart GirlsHigh School da ke Esigodini, sannan ɗalibai 55 daga makarantar Umzingwane High School. Kawo yanzu, ƙasar mai yawan al'ummar da ya haura milyan 15, mutum 1,525 aka tabbatar cutar korona ta yi ajalinsu. Sai dai a daidai lokacin da aka sake buɗe makarantun ƙasar, tsoron cewa…
Read More

zamfara: ‘Yan sanda sun daƙile yunƙurin harin ‘yan bindiga

Daga WAKILINMU 'Yan sanda a jihar Zamfara sun daƙile yunƙurin harin 'yan ta'adda a ƙauyen Yarkala a gundumar Rawayya da ke cikin ƙaramar hukumar Bunguɗu a jihar. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar jami'in, jami'ansu sun sunkuya aiki ne bayan da suka samu labarin shirin da 'yan bindigar suka yi don kai hari a ƙauyen Yarkala a Alhamis da ta gabata. “Bayan da muka samu kira, ba a yi wata-wata ba sai jami'anmu suka dira a yankin inda suka daƙile shirin 'yan…
Read More

Tsohon ɗan wasan Nollywood, Bruno Iwuoha ya rasu

Iwuoha Iwuoha ya bar duniya yana da shekara 68 bayan fama da ya yi da ciwon suga na tsawon lokaci. Shugaban Ƙungiyar 'Yan Wasan Fina-finai na Nijeriya, Ejezie Emeka Rollas, shi ne ya tabbatar da mutuwar marigayin. Kana ya yi amfani da wannan dama wajen jajanta wa iyalan marigayin game da rashin.
Read More

Sai da JAMB za a samu gurbin karatu a NDA – Hukumar Makaranta

Daga WAKILINMU Makarantar Horas da Sojoji ta Nijeriya (NDA) ta ce hankalinta ya kai kan wani rahoton ƙarya da ke ta karakaina a soshiyal midiya game da cewa an dakatar da JAMB a tsarin ɗaukar ɗalibai na '73 Regular Course'. Da wannan makarantar ta wayar da kan al'umma cewa lallai sai da shaidar jarabawar UTME za a iya samun gurbin karatu a '73 Regular Course', bayan kuma an samu adadin makin da hukumar JAMB ta tsayar. Daga nan, makarantar ta shwarci jama'a da su yi watsi da rahoton ƙaryar da aka yaɗa wanda ya nuna wai an dakatar da JAMB…
Read More

Imo: An sako sarki da fadawansa da aka yi garkuwa da su

Daga AISHA ASAS Bayanan da Manhaja ta samu ba da jimawa ba daga jihar Imo, sun nuna an sako Sarkin Umueze Nguru Aboh a ƙaramar hukumar Mbaise, Eze Charles Iroegbu yare da fadawansa. Talatar da ta gabata wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi garkuwa da Eze Iroegbu tare da wasu fadawansa su bakwai a kan hanyarsu ta zuwa wajen ɗaurin aure a ƙaramar hukumar Isiala Mbano. Binciken Manhaja ya gano cewa da sanyin safiyar wannan Asabar ne basaraken da fadawansa suka iso gida. Wata majiya ta kusa da fadar sarkin ta shaida…
Read More

Yajin aikin likitoci: Ya kamata Buhari ya gaggauta tsige Ministan Lafiya – Gololo

Minista Ehanire Daga FATUHU MUSTAPHA a Abuja Jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Barrister Garus Gololo, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta tsige Ministan Lafiya, Dr. Osagie Ehanire. Da yake zantawa da wakilinmu a Anbuja, Gololo ya ce 'yan Nijeriya ba su taɓa sa ran ganin likitoci sun tafi yajin aiki ba a irin wannan lokaci. Yana mai cewa Shugaba Buhari ya bada isassun kuɗaɗe don yaƙi da annobar korona har da ƙarin tallafin da aka samu daga hannun ɗaiɗaikun mutane. A cewar Gololo, "Me ya sa suka bari likitocinmu suka shiga yajin aiki? Gaskiya…
Read More