Editor

9513 Posts
Ramadan: Saraki Ya Ja Hankalin ‘Yan Kasuwar Nijeriya

Ramadan: Saraki Ya Ja Hankalin ‘Yan Kasuwar Nijeriya

Daga WAKILINMU Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya taya daukacin al’ummar Nijeriya da fadin duniya murnar fara azumin watan Ramadana. Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan dama wurin yin addu’ar Allah Ya dawo da zaman lafiya, hadin kai da bunkasar Nijeriya. Dakta Saraki ya bayyana haka ne a wata takardar manema labarai wacce Shugaban Sashen yada labarai naa ofishinsa, Yusuph Olaniyonu ya fitar a jiya. Ya ce, watan Ramadan lokaci ne da musulmi za su nemi kusanci ga mahaliccinsu kuma su kyautata alaka a tsakaninsu, musamman yin amfani da…
Read More
Rikicin ƙabilanci ya ci mutum biyar a kan iyakar Gombe da Adamawa

Rikicin ƙabilanci ya ci mutum biyar a kan iyakar Gombe da Adamawa

Daga AISHA ASAS Kimanin mutum biyar ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon rikicin ƙabilanci da ya auku a yankin garuruwan Nyuwar/Jessu masu maƙwabtaka da juna a kan iyakar Gombe da Adamawa inda ƙabilun Waja da Lunguda ke da zama. Wani ganau da ya shida faruwar rikicin ya bayyana cewa saɓanin ya faru ne sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin maharba daga Jessu da kuma Fulanin Lunguda a Adamawa, waɗanda tun ba yau ba babu alaƙa ta lumana a tskaninsu. Majiyar Manhaja ta ce yayin da maharban Jessu suka tafi daji farauta ne sai matasan Fulani suka tsinkaye su…
Read More
Ramadan 2021: Sau ɗaya aka amince maniyyata su yi Umura

Ramadan 2021: Sau ɗaya aka amince maniyyata su yi Umura

Daga WAKILINMU Ma'aikatar Kula da Harkokin Hajji da Umura ta Ƙasar Saudiyya ta bada sanarwar cewa sau ɗaya tak za a bai wa maniyyata damar gabatar da aikin Umura a wannan lokaci. A cewar jaridar Saudi Gazette, masu ibada na iya samun zarafin gabatar da salloli kulliyaumi a masallacin Ka'aba. Ma'aikatar ta ce maniyyatan da suka rigaya suka samu izinin yin Umura kada su sake shiga tsarin neman wani izinin har sai wa'adin izinin farko da suka samu ya ƙare. Yayin da kuma izinin gabatar da sallah a Masallacin Ka'aba zai yi amfani ne na yini guda wajen bai wa…
Read More
Perez ya zama shugaban Real Madrid karo na 6

Perez ya zama shugaban Real Madrid karo na 6

Daga BASHIR ISAH An sake zaɓen Florentino Perez ba tare da hamayya ba a matsayin shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid a karo na shida. Perez mai shekara 74, shi ne kaɗai ya kasance wanda ya tsaya takarar neman matsayin tun bayan da aka buɗe ƙofar takara. Ko a 2013 da 2017 Perez ya taki wannan matsayi bayan da ya yi takarar ba tare da wata hamayya ba. A matsayinsa na zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar, ana sa ran dattijon ya ja ragamar ƙungiyar ya zuwa 2025.
Read More
Legas: Ɗan sanda ya rasa aikinsa bayan da aka same shi da yinƙurin hallaka budurwarsa da bindiga

Legas: Ɗan sanda ya rasa aikinsa bayan da aka same shi da yinƙurin hallaka budurwarsa da bindiga

Daga UMAR M. GOMBE Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kori jami'inta Sergeant Eze Aiwansoba bayan da ta kama shi da laifin yinƙurin kisa sakamakon harbin da ya yi wa budurwarsa Joy Ndubueze a baki da bindiga. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, ya faɗa a wata sanarwar da ya fitar a Litinin da ta gabata cewa, baya ga korar da aka yi wa jami'in daga aiki an kuma gurfanar da shi a wata kotun majestare da ke Yaba bisa tuhumar kisa. A cewar Adejobi, “Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kori wani Sergeant Eze Aiwansoba daga…
Read More
Bauchi: Gwamna Bala ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai kuɗin jarrabawar JAMB/UTME, NECO

Bauchi: Gwamna Bala ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai kuɗin jarrabawar JAMB/UTME, NECO

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai 3,810 da suka samu sakamako mai kyau na auna fahimtar SSCE da aka yi musu kuɗin rajistar UTME. Haka nan, gwamnan ya amince ya biya kuɗin jarrabawar NABTEB ga ɗalibai 1,751 da ke ajin ƙarshe a makarantun fasaha da ke jihar, da kuma ɗalibai 499 daga makarantun koyon Larabci da ke shirin rubuta jarrabawar NBAIS bayan su ma an auna fahimtarsu. Bugu da ƙari, gwamnan ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai 11,580 da suka samu sakamako mai kyau na gwajin da aka yi musu,…
Read More
Kebbi: Wasu jigogin APC sun buƙaci a yi karɓa-karɓa game da kujerar gwamna

Kebbi: Wasu jigogin APC sun buƙaci a yi karɓa-karɓa game da kujerar gwamna

Daga FATUHU MUSTAPHA Wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Kebbi, sun yi motsi tare da ɗauko batun karɓa-karɓa game da sha'anin shugabancin jihar a tsakanin shiyoyin jihar. Da yake yi wa manema labarai bayani jim kaɗan bayan kammala ganawa da masu faɗa a ji na APC daga shiyoyin sanata na Kudu da Arewa na jihar, mai magana da yawun haɗakar kuma Kwamishinan Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Mohammed, ya ce manufarsu ita ce yadda za a tafi da kowa amma babban burinsu shi ne yadda za a riƙa kewayawa da keuerar gwamna ana…
Read More
Hajjin 2021: An yi wa maniyyata 2,837 rigakafin korona a Kaduna

Hajjin 2021: An yi wa maniyyata 2,837 rigakafin korona a Kaduna

Daga WAKILINMU A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajjin bana, Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Kaduna ta ce kawo yanzu an samu yi wa maniyyata 2,837 allurar rigakafin cutar korona a jihar. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar Riƙon Ƙwarya ta Hukumar, Hannatu Zailani, a wata ganawa da ta yi da manema labarai, tana mai cewa an soma gudanar da shirin yi wa maniyyatan rigakafin ne tun ran 6 ga Afrilun da ake ciki. Hannatu ta ce daga cikin maniyyata sama da 4,000 da jihar ke da su a bana, mutum 2,837 ne suka je…
Read More
Ahmed Musa ya shirya komawa Kano Pillars – Rahoto

Ahmed Musa ya shirya komawa Kano Pillars – Rahoto

Daga WAKILINMU Rahotanni sun tabbatar cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan kuma kyaftin a Super Eagles, wato Ahmed Musa, na shirin sake komawa ƙungiyar Kano Pillars don yin aiki na taƙaitaccen lokaci. Musa, ɗan shekara 28, ya kasance ba ya buga ma wata kulob wasa tun daga Otoban 2020, bayan kammala harƙallarsa da ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya, bayan kuma ya kasa samu ƙulla wata harka a Turai. Bayanai sun nuna ana sa ran tsohon ɗan wasan Leicester City ɗin zai yi aiki na ɗan lokaci tare da Kano Pillars. Kanawa na matuƙar martaba ɗan wasan tun bayan…
Read More

Majalisa ta gayyaci tsohon shugaban FMBN kan badaƙalar kwangilar bilyan N3

Daga AISHA ASAS Majalisar Dattawa ta hannun kwamitinta mai bin diddigin ayyukan gwamnati (SPAC), ta kirayi tsohon shugaban Bankin Bada Bashi (FMBN), Malam Gimba Yau Kumo, da ya bayyana a gabanta kan badaƙalar kwangilar Naira bilyan N3 da aka bayar. Kamar yadda rahoton da aka miƙa wa Ofishin Babban Jami'in Bincike na Ƙasa ya nuna, an bayar da kwangilar ne rukuni-rukuni har huɗu wanda hakan ya yi sanadiyar biyan kuɗi wuce abin da ya kamata a biya da Naira milyan N118,717,892. Bayanan Odita Janar wanda Shugaban Kwamitin Majalisar, Sanata Mathew Urhoghide (PDP Edo ta Kudu), ya bayyana wa manema labarai…
Read More