Babaji

5687 Posts

Atiku, Obi, Kwankwaso, Makinde da wasu sun haɗu Ibadan yayin babban taron ‘yan adawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu manyan ‘yan siyasar adawa sun isa birnin Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, domin halartar wani muhimmin taron ‘yan adawa da ake sa ran zai tattauna batutuwan siyasa da yiwuwar haɗin kai gabanin zaɓen 2027. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya tabbatar da zuwansa ta hanyar wallafa saƙo a shafukansa na sada zumunta da kuma nuna bidiyon da ke bayyana saukarsa a Filin Jiragen Sama na Ibadan a ranar Asabar. A cikin sakon, an ga Atiku cikin annashuwa tare da magoya bayansa da suka tarbe shi. Haka kuma, tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma…
Read More

Tsohon ɗan wasan gaba na Super Eagles ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar Super Eagles ta Nijeriya, Michael Eneramo, ya rasu sakamakon bugun zuciya yayin wani wasan sada zumunta a Jihar Kaduna. Hukumar Ƙwallon Kafa ta Ƙasa NFF, ta ce Eneramo mai shekaru 40 ya gamu da bugun zuciya ne mintuna biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan, lamarin da ya tilasta tsayar da wasan domin duba halin da yake ciki. Duk da cewa, an yi yunƙurin ba shi agajin gaggawa a filin wasan da kuma gaggauta garzayawa da shi zuwa asibiti, hakan bai sa ya samu tsira ba.…
Read More

Tinubu ya rantsar da Muttaqha Darma a matsayin ministan gidaje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Dakta Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon ministan gidaje da ci-gaban birane daga Jihar Katsina, bayan Majalisar Dattawa ta tantance shi. Ya maye gurbin Ahmed Musa Ɗangiwa, wanda ya yi murabus kwanan nan daga muƙamin. Shugaban, a taron wanda aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa, ya taya Dakta Darma murna bisa zuwa kan muƙamin a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubale wajen ci-gaban ƙasa. Tinubu ya shaida masa cewa ya shirya sauke nauyin da aka ɗora masa bisa jajircewa da ƙwarewa kamar yadda ya nuna…
Read More

NUPENG ta zaɓi sabon shugaba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗaya daga cikin amintattu na ƙasa na Ƙungiyar Ma'aikatan Fetur da Gas ta Ƙasa (NUPENG), Salimon Oladiti, ya zama sabon shugaban ƙungiyar. A ranar Juma'a ne aka zaɓi Olditi a muƙamin a yayin babban taron ƙungiyar karo na 6 da aka yi Legas. Haka kuma, an naɗa tsohon Shugaban reshen samar da Mai da Gas, Akin Oladejo a matsayin mataimakin shugaba.
Read More

Tsohon gwamnan Kogi ya yi nasara a shari’ar ɓatanci yayin da kotu ta umarci Sanata Natasha ta biya diyyar biliyan N1

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu a Lokoja ta umarci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ta biya diyyar Naira biliyan 1 akan wata ƙara da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya shigar. Kotun ta ce bisa la'akari da hujjojin da kuna ƙoƙarin warware matsaloli, ta yi hukuncin bai wa wanda ya shigar da ƙarar nasara. Mai Shari'a A. S. Ibrahim yayin hukuncin, ya bayyana cewa yayin kammala ƙarar, batutuwa biyu da aka yi nazari akan su sun nuna cewa wanda ya shigar da ƙarar ya yi nasara. Da fari dai akwai batun yaɗa kalaman ɓatanci akan wanda…
Read More

An kafa kotun soji don hukunta waɗanda aka zarga da yunƙurin juyin mulki

A yau Jumma'a ne ake gurfanar da sojoji 36 da ake zargi da yunkurin juyin mulki ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu, gaban Kotun Soji na musamman a Abuja, bayan da Hedikwatar Tsaro ta kafa kwamitin masu shari'a. Hedikwatar Tsaro ba ta yi wani sanarwa kan matakin ba, sai dai rahotanni na cewa kotun za ta yi zamanta a ɗakin taron manyan hafsohi na Scorpion da ke Asokoro a babban birnin tarayya Abuja a ranar 23 ga wataan Afrilu, bisa ga umarnin da AM Alechenu, Kwamandan sashin Garrison na Hedikwatar Tsaro ya sanya wa hannu. Umarnin, wanda aka sanya wa hannu…
Read More

Benuwai: Ɗan NYSC ya rasu bayan ‘yan bijilante sun lakaɗa masa duka a Buruku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ɗan hidimar ƙasa na Hukumar NYSC ya rasu bayan zargin lakaɗa masa duka da wasu 'yan bijilante suka yi a Ƙaramar Hukumar Buruku da ke Jihar Benuwai. Hukumomi sun tabbatar da kamawa da tsare waɗanda zargi da hannu a laifin inda ake sa ran gurfanar da su. Marigayin mai suna Ben Agir Une, wanda ɗan yankin Tongov ne a Ƙaramar hukumar Katsina-Ala, an kama shi ne a yayin wani sintiri cikin dare a yankin Anibros bisa zargin sa da a satar babur. Shaidu sun ce, akan haka ne aka lakaɗa wa Une dukan…
Read More

Tinubu ya amince da kaso 30 na sauƙaƙa bashi ga kamfanonin jiragen sama

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ragin kaso 30 na bashi da kamfanonin jiragen sama suka riƙe wa hukumomin sufurin jiragen sama, a wani yunƙuri na rage matsin tattalin a gare su yakin farashin fetur ya yi tashin gwauron zaɓi. Ministan sufurin jiragen sama da bunƙasa sararin samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana haka a wata takarda a juya Alhamis. ​Keyamo ya ce wannan ragi ya biyo bayan karɓar saƙon ne daga hannun Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa. Matakin ya zo ne bayan korafe-korafen da kamfanonin jiragen sama suka yi kan tsadar…
Read More

Ƙungiya ta yaba wa Gwamna Abba kan ɗaukar Murtala Garo a mataimakinsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Kano Alliance for Democracy and Development ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa hoɓɓasarsa wajen ciyar da dimukraɗiyya da shugabanci na gari gaba a Jihar Kano. Ƙungiyar, wadda manufarta ita ce ƙarfafa haɗin kai don samar da ci-gaba a Kano kuma cibiyar kasuwanci, siyasa da ɗaukar nauyi, ta ce Kano sama take da kowane mutum kuma al'amuran kwanan nan sun tabbatar da haka. Don haka ne ta jinjina wa gwamnan jihar bisa tabbatar da cewa shi ɗan dimukraɗiyya ne na gaskiya wanda hakan ya sa ya zaɓi maitaimakinsa ta bin hanyoyin da…
Read More

MTN za ta biya kwastomomi diyya bisa rashin ingancin sabis

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kamfanin sadarwa na MTN ya bayyana cewa zai bi umarnin Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) na biyan diyya ga masu amfani da layukansa da suka fuskanci matsalar rashin ingancin sabis. A sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, kamfanin ya ce duk kwastomomin da suka samu tangardar sadarwa a wasu yankuna za su ci gajiyar wannan diyya, musamman a lokutan da aka samu matsaloli a baya. Wannan ya biyo bayan matakin NCC na tilasta wa kamfanonin sadarwa su biya diyya idan sun kasa cika ka’idojin ingancin sabis (QoS). Hukumar NCC ta jaddada cewa bai…
Read More